Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta baiwa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) umarnin ta cire jam’iyyar ADC da sauran jam’iyyun siyasa 4 daga rajista saboda ci gaba da gazawa wajen cika ka’idodin aiki da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke wannan hukuncin a cikin karar da Kungiyar Tsoffin ‘Yan Majalisa na Kasa suka shigar, mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026.
Masu karar sun roki kotun ta yanke hukunci kan ko Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na da wajibcin Kundin Tsarin Mulki na cire jam’iyyun siyasa da suka gaza cika ka’idojin da Sashi na 225A na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ya tanada.
Karar ta dogara ne kan tanadin Dokar Zabe ta shekarar 2022 da ka’idojin INEC, wadanda aka ambata a matsayin masu karfafa bukatun Kundin Tsarin Mulki na rajistar jam’iyya da ci gaba da wanzuwarta.
Sauran jam’iyyun da abin ya shafa su ne APP, AA, AP da Zenith Labour Party.
Masu karar sun ce jam’iyyu biyar din sun ci gaba da nuna gazawa wajen cika ma’aunan Kundin Tsarin Mulki da ake bukata don ci gaba da rike rajistarsu. Ma’aunain sun hada da samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri’u a wata jiha a zaben shugaban kasa ko samun akalla kujera daya a zabe na kasa, na jiha ko na karamar hukuma.
Tsoffin ‘yan majalisun sun shaida wa kotu cewa ADC da sauran jam’iyyu hudun sun gaza a zaben gama gari na shekarar 2023 da kuma zabukan cike gurbi da suka biyo baya, inda suka gaza samun kujeru a manyan matakan gwamnati. Sun dage cewa ci gaba da wanzuwarsu a matsayin jam’iyyun siyasa da aka amince da su ya saba da doka kuma zai lalata mutuncin tsarin zabe.
Daga cikin abubuwan da aka roka, masu karar sun bukaci kotu ta bayyana cewa wajibi ne INEC ta cire irin wadannan jam’iyyu daga rajista da kuma tilasta wa hukumar ta yi hakan kafin shirye-shiryen zaben 2027 su kankama sosai.
Masuk arar sun kuma roki kotu ta hana jam’iyyu 5 din shiga zabe ko gudanar da ayyukan siyasa irin su kamfen, tarurruka da zaben fidda gwani, da kuma hana INEC amincewa da su ko mu’amala da su sai sun cika tanadin Kundin Tsarin Mulki yadda ya kamata.
Hukuncin na iya yin tasiri kan damar ‘yan takara daga jam’iyyun da abin ya shafa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda aka tsayar a jam’iyyar ADC gabanin zaben shugaban kasa na 2027 da kuma Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord Party.













































