Tsohon saurayin marigayiya Ummita, Dan Kasar China ya hallakata- Adamu Aminu

IMG 20220917 WA0171 598x430 1
IMG 20220917 WA0171 598x430 1

A safiyar ranar Asabar ne al’ummar Kano suka wayi gari da wani labari mai tayar da hankali na kisan wata Budurwa mai suna Ummita, wadda wani masoyinta mai shekaru 47 Dan kasar China Geng Quandong ya daba mata wuka.

Ummu-Khulthum Sani wadda ake Kira da Ummita, daba mata wukar da Masoyin nata, ya yi shi ne ya sabbaba mutuwar ta tun da sanyin safiyar Asabar.

Tuni dai kafafen sada zumunta na Internet suka cika da Hotunan marigayiya Ummita – wanda ke nuna kyakkyawar fuskarta dauke da murmushi mai kyalkyali, sanye da gyale mai ruwan hoda da bakar rigar sanyi, sanye da ‘yan kunne na zinari da Kuma sarkar wuya.

Allah ya jikanta da rahma yasa ta huta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, marigayiya Ummita ta dade tana cin gajiyar dimbin arziki daga dan kasar Chinan.

Rahotannin sun Kara da cewa lamura sun tabarbare har ta Kai ga marigayiya Ummita ta hana Geng Quanrong samun damar sanin gidanta, wadda hakan ne ya fusata shi har ya sha alwashin sanin inda take, wanda daga karshe ya yi nasarar aikata wannan danyen aikin.

Tunda Ummita ba ta nan, kuma wanda ake zargi da kisanta dan kasar China yana hannun jami’an ‘yan sandan Kano, kuma bai kamata a wuce gona da iri ba wajen yin karin bayani kan wannan lamari na kisan Ummita.

Amma abin da yakamata a fi mayar da hankali shi ne fadakarwa ga kowa da kowa cewa, babu wani babban bala’i da ya wuce sha’awa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here