Shugaba Bola Tinubu ya amince da daukar mutum 1,000 na masu tsaron daji a Jihar Oyo a matsayin wani bangare na matakan karfafa tsaro bayan sace dalibai da malamai a jihar.
An sanar da amincewar ne yayin ziyar tawagar Gwamnatin Tarayya da Mr Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya jagoranta zuwa garuruwan Ahoro-Esinele da Yawota kusa da Ogbomoso a karamar hukumar Oriire a ranar Lahadi.
Tawagar ta sanar da damuwar shugaban kasa kan sace dalibai da malamai na Community Grammar School, Ahoro-Esinele, Baptist Nursery and Primary School, Yawota da L.A. Primary School, Ahoro-Esinele a ranar 15 ga Mayu.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Mr Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar Onanuga, za a gudanar daukar masu tsaron dajin hadin gwiwar da Gwamnatin Jihar Oyo domin inganta tsaro a garuruwan da abin ya shafa da kewayensu.
Tawagar ta kuma sanar da shugabannin al’umma da ’yan majalisa cewa za ta isar da bukatarsu na kafa sansanin soja a yankin ga shugaban kasa don a yi la’akari da ita.
Tinubu ya kuma umarci wata runduna ta musamman ta tsaro da ke ceto ta hanyoyin na zamani ta kara kokari wajen tabbatar da sakin wadanda aka sace.
Sauran ‘yan tawagar sun hada da; Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, Babban Sufeton ’Yan Sanda, Olatunji Disu, Ministan Tsaro, Christopher Musa, da Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da sadarwa, Sunday Dare.
Yayin da yake jawabi ga mazauna yankin, Gbajabiamila ya ce Tinubu ya yi matukar damuwa da lamarin kuma ya umurci shugabannin tsaron kasar da su tabbatar da ceto wadanda aka tsare.
“Ya bayar da dukkan umarnin da goyon bayan da ya da hukumomin tsaromu ke bukata don samar da wannan manufa,” in ji shi.
Gbajabiamila ya tabbatar wa iyaye da mazauna garuruwan cewa aikin ceto zai dogara ne kan bayanan sirri kuma za a gudanar da shi cikin tsari don tabbatar da dawowar wadanda aka sace cikin koshin lafiya.












































