An kama mutane 8 da suka yi garkuwa da daliban Oyo -Tinubu

President Bola Ahmed Tinubu 1 750x430

Shugaba Bola Tinubu ya yaba da nasarar da aka samu na ceto daliban makaranta da malamai da aka yi garkuwa da su a garin Oriire da ke Ogbomoso, Jihar Oyo.

Ya yaba wa hukumomin tsaro bisa kokarinsu na kawo karshen aikin kwanaki 56 da suka yi ba tare da an rasa rai ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu yaba wa Sojoji, hukumar Tsaro ta DSS da ’Yan Sandan Najeriya bisa kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su tare da kama 8 daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su da ake zargi da kuma kawar da sauran mambobinsu.

Ya kuma nuna tausayawarsa ga yaran da malaman da aka ceto, iyalansu da ma kasa kaki daya kan radadin da lamarin ya haifar, yana mai cewa lamarin ya kasance abin takaici.

Tinubu ya ce wannan aikin ya samar da sauki ga iyalan da abin ya shafa da kuma kasa baki daya, yayin da ya yi alkawarin cewa wadanda suka aikata wannan laifi za su fuskanci shari’a.

Sanarwar ta ce, “Na yi matukar farin ciki cewa jami’an tsaro sun yi nasarar ceto dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su daga Oriire, Ogbomoso a Jihar Oyo a yau bayan wani aiki na soja, ’yan sanda da na leken asiri da aka yi wanda ya yi sanadiyyar kawo karshen ’yan ta’addan da suka aikata wannan mummunar aiki da kuma kama takwas daga cikinsu.

“Wannan nasarar aikin soja ta kawo karshen wannan matsala da ta kwashe sama da kwanaki 50, kuma ta kawo sauki ga kasar baki daya musamman ga iyalan da abin ya shafa.

“Gwamnati ta za ta tabbatar da an yi adalci ga wadannan yara da malamansu da kuma iyalin Mista Oyedokun, wanda ’yan ta’addan suka kashe shi cikin mugun hali.”

Shugaban ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Oyo bisa hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya a duk tsawon aikin ceto kuma ya roki jihar da ta karfafa tsaro a kusa da makarantu domin hana sake faruwar irin wannan lamari

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here