Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma’a ta sake dage yanke hukunci a kan shari’ar kwace kadarori da hukumar EFCC ta shigar kan kadarori 57 da ake da alaka da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, har zuwa ranar 15 ga watan Yuli.
Karar da aka sanya za a yanke hukunci a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ba ta ci gaba ba saboda mai shari’ar bata zauna ba.
Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa mai shari’ar ta sanya ranar 6 ga watan Yuli domin yanke hukunci tun ranar 26 ga watan Mayu.
Mai Shari’a Abdulmalik ta sanya wannan ranar ne bayan Lauyan EFCC, Jibrin Okutepa SAN, da Lauyan Malami da sauran wadanda ake tuhuma, Adedayo Adedeji SAN, sun gabatar da hujjojinsu tare da gabatar da muhawarar goyon baya da adawa da tsarin kwace kadarorin.
NAN ta ruwaito cewa hukumar yaki da rashawa ta bukaci a ba ta umarni na karshe don kwace kadarorin da ake zargi an same su ba bisa ka’ida ba.
Yayin gabatar da bukatar a ranar da aka dage shari’ar ta karshe, Okutepa ya shaida wa kotu cewa an shigar da bukatar a watan Fabrairu tare da goyon bayan shaidar rantsuwa mai sakin layi 47 da kuma gamsassun hujjoji 46.
Lauyan wanda ya ce bukatar na cikin Kundaye 3, ya roki kotu ta amince da bukatar.
Dogaro da takardun, ya bukaci kotu ta yanke hukunci cewa Malami da sauran wadanda ake tuhuma sun gaza wajen nuna dalilin da zai tabbatar da cewa an samu kadarorin ta halastacciyar hanya”.
Ya roki kotu ta ba da umarnin a kwace kadarorin har abada a ba gwamnatin tarayya.
A nasa bangaren, Adedeji ya ce an shigar da wannan bukata a ranar 27 ga Fabrairu tare da goyon bayan shaidar rantsuwa mai sakin layi 109 da Malami da kansa ya bayar.
Ya ce an shigar da shaidar rantsuwar ne domin nuna dalilin da zai sa ba za a ba da umarnin karshe na kwace kadarorin ba.
Adedeji ya roki kotu ba wai ta soke umarni na wucin gadi na baya ba kadai, har ma ta yanke hukunci cewa wadanda ake tuhuma sun nuna cewa ba a samu kadarorin ne daga kudaden laifi ba”.










































