Dakarun rundunar Operation HADIN KAI sun kama mutane 12 da ake zargi da taimakawa da kayayyaki da hada baki da ‘yan ta’addan ISWAP/JAS a ayyuka daban-daban a fadin Jihar Borno.
Wani rahoton aiki da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata a Abuja ya ce sojojin Bataliya ta 135 na Special Forces hadin gwiwa da Civilian Joint Task Force da ‘yan banga, sun kama mutane 10 a Kurnari.
Rahoton ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da suke kan hanyar zuwa Kasuwar Miringa da shanu 5, kekuna 2, wayoyin hannu 9, jakunkuna 2, wuka da Naira 12,600.
Ya kara da cewa ana tsare da wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato a hannun sojoji domin ci gaba da bincike.
Rahoton ya kuma ce a wani aikin daban, sojojin Bataliya ta 149, hadin gwiwa da hybrid forces da CJTF, sun kama wani da ake zargin mai taimakawa ‘yan ta’adda ne a Kauyen Zowo da ke Karamar Hukumar Gubio.
“An kwato lita 125 na man fetur PMS, wata wayar hannu da sauran kayayyaki daga hannun wanda ake zargin.
“Rahoto ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin cewa yana daukar kayayyaki ne ga ‘yan ta’adda da ke aiki a yankin Binduldul-Kareto,” in ji shi.
Rahoton ya kara bayyana cewa sojojin Brigade ta 19 da CJTF sun kama wani da ake zargin dan leken asirin ‘yan ta’adda ne a Monguno.
A cewar rahoton, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana taimakawa da bayar da labarin zirga-zirgar sojoji ga ‘yan ta’addan da ke aiki a yankin Kekeno-Monguno.
Ya kuma kara da cewa sojojin da ke sintiri a Mallam Fatori sun samu bam din mortar mai girman 60mm da bam din RPG da aka yi watsi da su, ana zargin ‘yan ta’addan ne suka bar su.
“ Kwararrun Jami’an Explosive Ordnance Disposal sun tabbatar da kwato bamabaman da ba su fashe ba cikin aminci,” in ji rahoton.













































