An hana dan wasan tsakiyar tawagar Black Stars ta Ghana, Thomas Partey, shiga kasar Kanada a wasan farko da tawagarsa zata buga a Gasar Cin Kofin Duniya.
Athletic ta rawaito cewa gwamnatin Kanada ta ki baiwa dan wasan da ya taba taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal biza saboda zargin tuhumar fyaden da ake yi masa a kasar Birtaniya.
Kanada na da dokokin shige da fice masu tsauri wadanda ke hana ‘yan kasashen waje da ake tuhuma da manyan laifuka na aikata laifi shiga kasar.
Black Stars har yanzu suna sansanin horo a Boston a Amurka, kuma za su tafiya zuwa Kanada nan ba da jimawa ba domin wasan su na farko na Kofin Duniya da Panama.
Partey zai iya yin atisayetare da abokan wasan sa a kasar Amurka, amma za a hana shi ketare iyaka zuwa Kanada domin wasan da za a buga a filin BMO na Toronto a ranar 18 ga Yuni.
Partey ya bar Birtaniya a 2025 ya koma Villarreal FC a Spain bayan tuhumar da aka yi na ce ya cin zarafin wasu mata yayin da yake London.
Dan wasan Ghanan a yanzu ana tuhumar sa da laifuka 7 na fyade da guda faya na cin zarafin da suka shafi mata 4.
Dan wasan tsakiya ya ce bai aikata laifin ba, ya kuma ce “ba shi da laifi” ga dukkan tuhume-tuhumen.
Babbar kotun Birtaniya ta dage sauraron karar makonni 8 da farko za a yi a kotun Southwark Crown zuwa watan Yuni 2027.













































