Sakataren ƙasa na jam’iyyar NNPP, Ogini Olaposi, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai samu damar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Olaposi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a birnin Lagos.
Ya ce, tikitin shugaban ƙasa na NNPP a 2027 zai kasance a buɗe ga sahihan mambobin jam’iyyar da ke sha’awar tsayawa takara a zaɓukan shugaban ƙasa da sauran muƙamai.
Ya ce Kwankwaso, wanda ya yi amfani da tikitin NNPP a zaɓen 2023, ba zai sake samun wannan dama ba a 2027 sakamakon sabani da rikice-rikicen da suka ɓarke tsakanin jam’iyyar NNPP da ƙungiyar Kwankwasiyya bayan kammala zaɓen.
Olaposi ya bayyana cewa NNPP ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da ƙungiyar Kwankwasiyya a shekarar 2022, amma yarjejeniyar ta ƙare ne bayan kammala zaɓukan, tare da nuna cewa ayyukan adawa da jam’iyya da wasu mambobin ƙungiyar suka yi bayan zaɓen shugaban ƙasa sun kai ga korar manyan jagororinsu, ciki har da Kwankwaso da Buba Galadima, kuma ba a janye hukuncin korar ba.
Karanta: Yadda wani minista ya raina ni a taron majalisar zartarwa ta ƙasa – Lai Mohammed
Ya ƙara da cewa tikitin NNPP na 2027 a buɗe yake ga dukkan mambobi, sabanin 2023 da aka bai wa Kwankwaso shi kaɗai, yana mai cewa a halin yanzu akwai masu sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa daga cikin jam’iyyar, har da wasu daga mambobin NNPP da ke ƙasashen waje, tare da buɗe ƙofa ga haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun da ke da irin akida ɗaya.
Sakataren jam’iyyar ya bayyana cewa abin dariya ne Kwankwaso yana ikirarin cewa duk jam’iyyar da zai koma dole ta ba shi tikitin shugaban ƙasa, yana mai cewa Kwankwaso ba shi da ƙarfin jan hankalin ƙasa baki ɗaya kamar Shugaba Bola Tinubu.
A cewar sa, tasirin Kwankwaso a jihar Kano an cika yawaita shi, duba da yadda manyan jiga-jigan ƙungiyar Kwankwasiyya suka riga suka fice zuwa jam’iyyar APC.
Olaposi ya ƙara da cewa ƙarfin APC da Shugaba Tinubu a 2027 ya ta’allaka ne kan ayyukan da suka aiwatar a matsayin jam’iyyar da ke mulki, ba wai kan tasirin mutum ɗaya ba, yana mai cewa tasirin Kwankwaso a matsayin tsohon gwamnan Kano ya ragu sosai kuma ba zai iya yin tasiri kan ƙuri’un Tinubu a Kano a 2027 ba.
Ya kuma buƙaci jam’iyyun siyasa da ke sha’awar haɗin gwiwa da NNPP a 2027 su bi hanyoyin doka ta hanyar kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar da kotuna suka amince da shi.
Ya kuma jaddada cewa Kwankwaso da ƙungiyarsa har yanzu suna cikin jerin waɗanda aka kora daga jam’iyyar kuma ba su da ikon tattaunawa ko yanke shawara a madadin NNPP.













































