IPAC ta yi watsi da yunkurin kawo Yusuf Kolo a matsayin sabon kwamishnan ‘yan sandan Kano

IGP Usman Baba 1
IGP Usman Baba 1

Gamayyar jam’iyun dake karkashin IPAC, reshan jihar Kano, ta yi watsi da yunkurin rundunar ‘yan sandan Najeriya, na kawo tsohon kwamandan  rundunar dake yaki da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane, wadda aka fi sani da SARS, wato Kolo Yusuf, a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sandan Kano.

A wani taron manema labarai da IPAC tayi ranar Litinin, wanada mataimakin shugaban gamayyar jam’iyun da ke karkashin IPAC, wanda shine kuma shugaban jam’iyyar Zenith Labour Party, Isa Nuhu Isa Danfulani  ya jagoranci taron, tare da sauran shuganbanin jam’iyu goma sha biyar, sun zargi gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da lallaba shugaban ‘yan sandan Najeriya da ya kawo masa Kolo Yusuf a matsayin sabon kumandan ‘yan sandan Kano.

Solacebase ta rawaitu cewa, kamar yace rahoton da jiridar Daily Nigerian ta bayar, cewa shugaban ‘yan sandan na kasa baki daya, wanda yanzu haka ya yi tafiya, amma ya tabbatar wa da gwamnan Kano cewa da zarar ya dawo daga tafiyar tasa zai kawo Kolo Yusuf Kano.

IPAC ta zargi Kolo da hannu wajan kasha wani dan asalin Kano, mai suna Abdullahi Alfa, wanda jami’an na SARS suka lakada masa na jaki, har sai da ya dai na nunfashi, kuma wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Kano, ta tabbatar da cewa Kolo yana da hannu wajin kisan.

Yayin taron manema labaran da IPAC ta yi, ta labarta kokarin da mirgayi sarkin Kano, Alh Ado Bayero tare da mirgaye Bashir Tofa  suka yi, wajan ganin an dauke Kolo daga Kano, sabo da rashin imanin da yake aikatawa.

IPAC ta kara da cewa  kawo Kolo Kano, zai iya haifar da rashin zaman lafiya, da kuma haifar da magudin zabe.

Gamaryar jam’iyun sun nemi da shugaban ‘yan sandan daya kawo kwararre wanda ya san aikin sa, ba kamar Kolo ba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here