Tinubu ya tabbatar da kashe babban kwamandan ISIS a tafkin Chadi

Bola Tinubu Tinubu Kano

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da kashe wani babban kwamandan kungiyar Islamic State, Abu-Bilal Al-Manuki, wanda aka fi sani da Abu-Mainok, a wani farmaki na hadin gwiwa da sojojin Najeriya da na Amurka suka gudanar a yankin tafkin Chadi don yaki da ta’addanci.

A cikin wata sanarwa da ta fito daga Aso Villa, Tinubu ya bayyana farmakin a matsayin babbar nasara a yaki da ta’addanci da ake yi, kuma misali ne mai karfi na hadin gwiwar tsaro mai inganci tsakanin Najeriya da Amurka.

A cewar shugaban, an kai farmakin ne cikin dare ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Sojojin Najeriya da Sojojin Amurka, inda aka kashe Al-Manuki tare da wasu manyan mukarrabansa a lokacin da aka kai farmaki kan harabar gidansa a yankin tafkin Chadi.

Tinubu ya ce farmakin ya yi mummunar illa ga kungiyar Islamic State kuma ya sake tabbatar da kudirin Najeriya na ci gaba da matsa wa kungiyoyin ta’addanci da ke aiki a cikin da kewayen kasar.

“Zakakuran jami’an sojojin Najeriya, da ke aiki tare da Sojojin Amurka, sun kai wani farmaki na hadin gwiwa wanda ya yi mummunar illa ga kungiyar Islamic State,” in ji shugaban.

“Bayanan farko sun tabbatar da kashe wanda ake nema ruwa a jallo, babban shugaban IS, Abu-Bilal Al-Manuki, wanda kuma aka fi sani da Abu-Mainok, tare da wasu mukarrabansa.”

Shugaban ya bayyana godiyarsa ga Amurka bisa goyon bayan da take bayarwa wajen ciyar da manufofin tsaro da muke da shi tare, yayin da ya gode wa Shugaban Amurka Donald Trump musamman kan jagorancinsa da hadin gwiwarsa.

Ya kuma yaba wa jami’an soji na kasashen biyu bisa kwarewa da jaruntakar da suka nuna yayin aikin, yana mai bayyana fata cewa za a kara daukar matakai masu karfi a kan sansanonin ta’addanci a fadin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here