Dan Shekara 30 ya janye daga takarar Majalisar Wakilai ta Kaduna

Mahmud Buba 750x430

Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Al-ajabin Zazzau, ya janye daga takarar Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Sabon Gari a Majalisar Wakilai a jam’iyyar APC.

Buba ya sanarda janyewar tasa ne a cikin wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar na Jihar Kaduna kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Asabar. Inda yace shawarar ta biyo bayan kokarin sulhu da shugabannin jam’iyya suka yi da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

“Da fatan za ku karbi wannan wasika a matsayin sanarwa ta hukuma cewa na janye daga takarar Dan Majalisar Sabon Gari, Majalisar Wakilai, daga yanzu,” in ji wani bangare na wasikar.

Ya bayyana hukuncin a matsayin mai wahala amma mai mahimmanci saboda hadin kai da nasaarr jam’iyya kafin zabe.

“Na gode wa jagoran jam’iyyarmu, Mai Girma Sanata Uba Sani, CON, da shugabancin jam’iyya a Jihar Kaduna bisa damar da suka ba ni na shiga tsarin zaben fidda gwanin.

A cewarsa, goyon bayan dan takara guda ya zama abu mai muhimmi ga APC a gabanin zabe da kuma ci gaban karamar hukumar da Jihar Kaduna.

“Ina sake tabbatar da cikakkiyar biyayya da sadaukarwata ga APC, janyewata ba alamar rauni ba ce illa sadaukarwa don amfanin jam’iyya gaba daya. Ina tabbatar muku cewa zan ci gaba da kasance mai biyayya ga jam’iyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here