Jami’an tsaro sun kara kama barayi uku da ake zargi da satar wayar wuta a filin jirgin sama na Legas- FAAN

FAAN 1
FAAN 1

Hukumar dake kula da tashi da saukar jirage ta kasa (FAAN) ta ce jami’an tsaro sun kama mutane uku da ake zargi da satar wayar wuta a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta FAAN, Abdullahi Yakubu-Funtua ya fitar ranar Juma’a.

Sanarwa ta ce an kama wadanda ake zargi ne a makarantar bada horo ta hukumar ranar Juma’a.

Sanarwa ta kara da cewa jami’an tsaro na hadin gwiwa ne suka yi nasarar kama wadanda ake zargin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here