Tawagar gwamnatin jihar Kano ta kai ziyarar ta’aziyya zuwa jihar Sokoto dangane da rasuwar Sardaunan Sokoto, Alhaji Abubakar Alhaji a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Tawagar wanda mataimakin gwamna, Alhaji Murtala Sule Garo, ke jagoranta, tare da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isa Umar, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa da Kwamishinar Al’adu da Yawon Bude Ido, Hajiya Aisha Lawan Saji, tare da wasu manyan jami’an gwamnati, sun kai ziyara gidan marigayin Sardaunan Sokoto inda suka isar da sakon ta’aziyyar Gwamna Yusuf ga iyalansa.
Babban dan marigayin, Aminu Abubakar Alhaji, ne ya tarbe su, inda ya godewa gwamnan bisa nuna jaje da goyon baya.
Daga nan tawagar ta kai ziyara Fadar Sarkin Musulmi domin isar da sakon ta’aziyyar Gwamna Yusuf ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III.
Sarkin Musulmi ya godewa Gwamna Yusuf bisa wannan kyakkyawar dabi’a, inda ya ce hakan na nuni da hadin kai da ’yan’uwantaka da ke tsakanin al’ummar Arewacin Najeriya.
Daga baya tawagar ta wuce zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto inda mataimakin gwamna da Sakataren Gwamnatin Jihar suka tarbe su.
Sun isar da sakon ta’aziyar Gwamna Yusuf ga gwamnati da al’ummar jihar Sokoto kan wannan rashi.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin Sardaunan Sokoto, Ya ba shi Aljannatul Firdaus, kuma Ya ba iyalansa, Majalisar Sarkin Musulmi da al’ummar Sokoto hakurin jure wannan babban rashi.












































