Gwamnatin tarayya ta dage takunkumin hana zirga-zirgar da ta sanyawa kamfanin jiragen sama na Emirates, a cewar ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.
Idan za a iya tunawa, Najeriya ta dakatar da Emirates daga shawagi ko fita daga cikin kasarta bayan da kamfanin ya sanya wasu ƙa’idoji na gwajin COVID-19 ga fasinjoji daga Najeriya a cikin watan Maris.
Amma Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya sanar da dage takunkumin da aka sanya wa kamfanonin jiragen sama na Emirates a ranar Juma’a, a Abuja.
Yace “A yau mun sami tattaunawa da Emirates tare da cire wasu sharuɗɗan yin balaguron sabida iftila’in da ya ke faruwa”.
“Bayan hakan ya zama dole a dage haramcin da aka yi wa Emirates.
Wannan dage haramcin da ya biyo bayan samun matsaya daga tattaunawa tsakaninmu da su.” inji shi













































