Kotu ta umurci NBTE da ta buɗe kadarorin Mangal da ta kulle a Abuja

Court High
Court High

Wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya ta umurci hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa NBTE da ta buɗe gidan Murjanatu da ke gini mai lamba 1405 Cadastral A 05, Maitama Abuja mallakin D. B Mangal Nig. Ltd, a daidai lokacin da ake sauraren korafin da aka shigar a gabanta

Masu shigar da karar, kamfanin D. B. Mangal Nig. Ltd. ya gurfanar da wandanda yake kara da suka hada da Babban Lauyan Tarayya, Hukumar Tsaro ta Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da kuma Hukumar ta NBTE a Kotu kan laifin keta alfarmar kadarorinta ba bisa ka’ida ba, wato Murjanatu house da ke Lamba 1405 Cadastral A 05, Maitama Abuja.

An ba da umarnin ne bayan sauraron karar da aka shigar a ranar 19 ga Nuwamba, 2021 da kuma sauraron Barr. Ahmed Raji SAN tare da Peter Nwatu wadanda sune lauyoyin mai shigar da kara.

A cikin umarnin da mai shari’a Yusuf Halilu ya bayar a ranar 25 ga watan Nuwamba, kotun ta umurci wanda ake kara na hudu da ya ba da damar bude gidan Murjanatu da ke Lamba 1405 Cadastral A 05, Maitama Abuja.

Hakazalika kotun, ta umurci bangarorin da ke karar da su dakata a halin yanzu kafin su kwace kadarorin wanda ake kara ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Halilu, ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga Disamba, 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here