Kwamitin Aiki na Riko na Kasa (INWC) na jam’iyyar (PDP) ya bayyana cewa zai daukaka kara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta yanke a ranar Juma’a, wanda ta ki amincewa da shugabancin Tanimu Turaki a matsayin halataccen shugabancin jam’iyyar.
Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP, karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara, tare da wasu mambobin da suka kafa jam’iyyar, sunka kai kara gaban kotun suna neman a baiwa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) umarnin ta amince da kwamitin INWC karkashin Turaki.
Sai dai, Alkalin Kotun, Justice Salim Olasupo Ibrahim, ya yi watsi da karar bayan ya amince da hujjojin kariya da wadanda ake kara suka gabatar.
Wannan ci gaba na nufin cewa INEC za ta tsaya kan matsayarta da ta yanke na amincewa da Kwamitin Aiki na Kasa (NWC) na jam’iyyar karkashin jagorancin Abdulrahman Mohammed, wanda Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ke marawa baya.
Tuni dama INEC ta bai wa bangaren PDP mai goyon bayan Wike lambobin sirri domin dora sunayen ‘yan takararsu na shugaban kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa na zaben 2027 a shafinta na intanet, aikin da aka riga aka kammala a ranar 14 ga watan Yuli.
Da yake mayar da martani kan hukuncin a daren ranar Juma’a, kwamitin INWC karkashin Turaki ya ce zai daukaka kara ne saboda ya yi amar cewa hukuncin kotun na da matsala.
“Yayin da muke girmama hukuncin kotun shari’ar, muna ganin cewa ya saba wa hukunce-hukuncen da kotunan daukaka kara da na koli suka yanke a baya, hakan ya sa masu shigar da karar ba su da wani zabi illa su daukaka kara kan hukuncin da kuma matakan da aka dauka a kai. Don haka, masu shigar da karar sun riga sun umarci lauyoyinsu da su dauki matakai na gaggawa domin daukaka kara kan wadannan umarnin da kuma hukuncin baki daya,” in ji Sakataren Yada Labarai na Kasa, Kwamared Ini Ememobong.
Bangaren ya nuna cewa yana tsaye ne a kan tafarkin gaskiya kuma lallai zai yi nasara wata rana, inda ya yi nuni da zargin yin amfani da babban tasirin siyasa da na kudi.











































