Majalisar Dattawa ta tabbatar da tsohon mai taimakawa shugaban majalisar a matsayin kwamishinan hukumar zabe

Etekarnba Umoren
Etekarnba Umoren

Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Etekarnba Umoren a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jihar Akwa Ibom.

Umoren ya taba rike mukamin shugaban ma’aikata ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a lokacin yana ministan harkokin Neja Delta.

Tsohon mataimakin ya kuma kasance fitaccen dan jam’iyyar APC ne a jihar Akwa Ibom.

Nadin nasa dai ya haifar da cece-kuce, inda kungiyoyi daban-daban musamman na masu fafutukar kare hakkin jama’a suka nemi Shugaba Bola Tinubu da ya soke nadin nasa.

Sai dai shugaban kasar a cikin wata wasika da aka karanta ranar Talata, ya bukaci majalisar dattawan da ta tabbatar da Umoren da sauran wadanda aka tura sunayen su domin a nada su.

Yanzu haka dai, an tabbatar da Umoren tare da Isah Shaka Ehimeakne daga jihar Edo da Oluwatoyin Babalola daga jihar Ekiti sai Abubakar Ahmed Ma’aji daga jihar Gomb) da Shehu Wahab daga jihar Kwara da Aminu Kasimi Idris daga jihar Nasarawa da kuma Mohammed Abubakar Sadiq daga jihar Neja.

Sauran mutum ukun da za’a nada din daga jihohin Rivers da Zamfara da Legas wato Anugbum Onuoha da Abubakar Fawa Dambo da kuma Bunmi Majalisar dattawan ta kuma tabbatar da nadin Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here