Jami’ar kimiyar sufuri ta Daura ta shiga cikin jerin jami’o’in kasar nan da hukumar Jamb ke bada gurbin karatu a cikin su

FUTD
FUTD

Shuagaban sabuwar Jami’ar nazarin aikin tafiye-tafiye ta gwamnatin tarayya dake garin Daura a Jihar Katsina wato Federal University of Transportation, Daura (FUTD), Farfesa Umar Adam-Katsayal, yace yanzu haka jami’ar ta shiga cikin jerin jami’o’in kasar nan da hukumar shirya jarabawar Jamb ke bada gurbin karatu a cikin su.

Shugaban Jami’ar ya bayyana hakan ne a zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ranar Laraba 2 ga watan Nuwambar, 2023 a Katsina.

A cewar Farafesa Umar Adam-Katsayal, yana yi wa Daliban dake bukatar sauya Jami’o’in da suka cike a jarabawar JAMB, albishir cewa yanzu za su iya sauyawa zuwa sabuwar jami’ar ta gwamnatin tarayya dake garin Daura a Jihar Katsina.

Yace duk daliban dake da burin yin karatu a fannin harkokin tafiye-tafiye sais u hanzarta ziyartar shafin hukumar JAMB domin sauya jami’ar da suka cike a baya zuwa sabuwar.

Farfesa Adam-Katsayal ya kuma zayyana wasu fannonin karatu da jami’ar ke yi da suka hadar da B.Eng. Civil Engineering da B.Eng. Electrical and Electronics Engineering da B.Eng. Mechanical Engineering.

Sauran sun hadar da B.Eng. Mechatronics Engineering da B.Eng. Railway Engineering da B.Eng. Highway Engineering da B.Sc. Aviation Management sai B. Sc. Transport Management da kuma B.Sc. Logistics and Supply Chain Management.

Karin wasu fannonin karatun da jami’ar ke yi sun hadar da B.Sc. Maritime Safety and Environmental Administration da BSc. Railway Transport Management da B.Sc. Sea Port and Dry Port Management sai B.Sc. Inland Waterways Safety and Environmental Administration da kuma B.Sc. Maritime Economics.

Farfesa Adam-Katsayal ya kuma bayyana cewa anbin da ake bukiata domin samun gurbin karatu a jami’ar shi ne Credit biyar a jarabawar kammala sakandire.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here