JAMB ta yi watsi da takardar sakamakon jarrabawar UTME na bogi mai maki 394 da ke yawo a shafukan sada zumunta

Jamb 1 1

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta bayyana cewa takardar sakamakon da ke yawo, wadda ke nuna cewa wata daliba daga Jihar Cross River ta samu maki 394 a jarrabawar UTME ta 2026, na bogi ne.

Sakamakon, wanda ya karade shafin X, wanda wani amfani da sunan @Onsogbu ya wallafa, wanda ya nuna cewa wata daliba mai suna Okon Winniefred Sampson ta samu maki 394 cikin 400.

Okon Winnifred Sampson, wata yarinya daga Jihar Cross River, ta nuna kwarin bajinta a jarrabawarta ta UTME, inda ta samu maki 394 cikin 400.

“Dalibar ta samu nasarar samun  maki 96 a Turanci da 99 a Biology da 98 a Chemistry sai kuma 99 a Physics… lallai gagarumar nasara ce a fannin ilmi. Ina son haka,” in ji Onsogbu.

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya bayyana takardar a matsayin ta bogi kuma ya bukaci jama’a su yi watsi da ita.

“Wata takardar sakamako da ake yadawa a shafukan sada zumunta, da ke nuna cewa wata daliba ta samu maki 394 a jarrabawar UTME ta shekarar 2026, ba ta gaskiya bace. Abin mamaki ne yadda ake yada irin wannan kirkirarran abun a tsakanin ‘yan Najeriya masu ilimi,” in ji sanarwar.

Benjamin ya bayyana cewa sakamakon UTME amfaninsa shi ne dalibi ya ga abin da ya samu ne kawai, ba don yawo a matsayin takarda ko a rabawa ba, yana mai cewa takardar da ake magana a kai an kirkire ta ne.

“Da farko, Hukumar ta bayyana a sarari cewa sakamakon UTME ana iya gani ne kawai. Takardar da ake yaɗawa ta fito ne daga wani tsarin takarda da aka kirkira, wanda shi kadai ya isa ya nuna cewa ba sahihi ba ne,” in ji shi.

Ya kuma nuna cewa lambar rajista da ke cikin sakamakon ma ta bogi ce, domin JAMB bata amfani da irin ta.

Ya kuma kara da cewa, lambobin rajista na hukumar ana samar da su ne ta hanyar tsari kuma ba sa bin tsarin ‘20269’ kamar yadda aka gani a takardar bogin. Akwai sabani da yawa a ciki, ko da a kallo daya, ke nuna cewa sakamakon na bogi ne.

Hukumar ta bukaci jama’a su dogara ga hanyoyin sadarwa na hukuma kawai don samun sahihan bayanai.

Benjamin ya kuma shawarci jama’a da su yi watsi da wannan sakamakon na bogi kuma su dogara ga hanyoyin sadarwa na hukuma kawai don samun sahihan bayanai. Duk sakamako a halin yanzu ana iya kallo ne kawai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here