2027: Makinde ya ayyana tsohon Shugaban DSS Daura a matsayin mataimakinsa

Oyo State Governor Seyi Makinde (1)

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), Seyi Makinde, ya zabi tsohon Babban Daraktan Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Lawal Daura, a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

An bayyana Daura, wanda ya jagoranci hukumar ta SSS daga shekarar 2015 zuwa 2018, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na Makinde a yayin babban taron kasa na jam’iyyar da aka gudanar a dandalin Rilwan Adamu Square da ke Bauchi a ranar Alhamis.

Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Oyo, Prince Dotun Oyelade ya fitar, inda ya bayyana cewa Makinde ya zabi tsohon shugaban hukumar leken asirin ne cikin sani domin magance matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a kasar.

“Abokin takararsa na Shugaban Kasa shi ne Alhaji Lawal Musa Daura, tsohon Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) tsakanin 2015 da 2018, wanda ya ce an zabe shi ne cikin sani domin warware matsalar tsaron da kasar ke fama,” in ji sanarwar.

Daura ya yi aiki a matsayin babban daraktan SSS a karkashin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kafin a cire shi daga mukaminsa a shekarar 2018.

An zabi Makinde a hukumance a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM a wajen taron, inda ya yi amfani da damar wajen yin alkawarin aiki tare da ‘yan siyasa masu ra’ayi daya da shi domin ci gaban kasa.

“Dan takarar shugaban kasa na APM ya ce zai yi aiki tukuru tare da ‘yan siyasa masu ra’ayi guda domin tabbatar da ganin an samu ingantacciyar Najeriya a shekarar 2027,” in ji sanarwar.
Gwamnan na Jihar Oyo ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya yaki fatara tare da inganta rayuwar miliyoyin ‘yan Najeriya, yana mai cewa matsalolin tattalin arziki na baya-bayan nan sun tsananta ne saboda rashin kyawun manufofi.

“Gwamna Makinde ya ce ya shirya tsaf domin fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci, wanda ya daidaita kasar musamman a cikin shekaru uku da suka gabata sakamakon manufofin da ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba,” in ji Oyelade.

Bugu da kari, Makinde ya bayyana cewa an zabi jihar Bauchi don gudanar da taron ne saboda muhimmancinta na tarihi a matsayin jihar da tsohon Firaministan Najeriya na farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, ya fito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here