Zaben Jihar Osun: Kotun sauraron kararrakin zabe ta fitar da koken APC da PDP kan sake zaben Adeleke

APC and PDP Tribunal 750x430

Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnatin Jihar Osun ta fitar da koke-koke 2 da Jam’iyyun APC da PDP suka shigar, suna kalubalantar sake zaben Gwamna Ademola Adeleke.

An kafe kararrakin masu kwanan wata 5 ga Satumba 2026, allolin sanarwa na sakatariyar kotun da ke Osogbo a ranar Litinin, wanda hakan ya zama manuniya na fara sauraron takaddamar da ta taso daga zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta a hukumance.

Wannan ya biyo bayan tabbatar da Sakataren Kotun, Pefe Belemore, cewa an shigar da koke-koken kalubalantar sakamakon zaben.

Belemore ya ce a baya cewa za a manna sanarwar da ta dace a allolin kotun kafin karfe 12 na rana a ranar Litinin.

Da aka fara zaman kotun da safe, Belemore na cikin kotu tare da sauran jami’an sakatariyar yayin da ake shirin fara aiki.

Jan’iyyun APC da PDP na kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa Gwamna Adeleke damar sake zama gwamna a wani wa’adin.

Ana sa ran fitar da koke-koken zai bude hanya ga mika takardu ga bangarorin da abin ya shafa da kuma ci gaba da sauraron karar a gaban kotun.

Koken APC, mai lamba EPT/OS/GOV/01/2026, dan takarar su Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, ne ya shigar kan Adeleke, Jam’iyyar Accord da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Koken PDP, mai lamba EPT/OS/GOV/02/2026, wanda Adebayo Olugbenga Adedamola, ya shigar kan Adeleke, INEC da Jam’iyyar Accord.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here