Matatar Mai ta Dangote ta sanar da mafi karancin hannun jari na IPO

Dangote 692x430

Babban Shugaban Gudanarwar rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetir da Masana’antar Petrochemicals na Dangote ya tsara mafi karancin adadin hannun jari da jama’a za su iya yi (IPO) na farko shi 10 na gama gari, wanda jimillar kudin farashinsa ya kama Naira 5,250.

Dangote ya bayyana hakan ne a wajen taron sanya hannu kan yarjejeniya da aka gudanar a Legas a ranar Litinin.

Ya ce IPO din ya kunshi bayar da biliyan 4.1 na hannun jari na yau da kullum, kowanne yana da darajar dala 0.000013, kuma ana sayar da shi akan Naira 525 ga kowanne hannun jari.

“A cikin wannan IPO, muna niyyar tara kusan sama da Naira tiriliyan 2, wanda ina ganin kadan ne, a farashin Naira 525, tare da mafi karancin sanya hannun jari 10 kawai domin tallafawa fadada kamfanin tace man mu,” in ji shi.

Ya ce ba kawai niyyar kudaden za a yi amfani da su wajen fadada kamfanin tace man ba, har ma domin tabbatar da cewa direbobinmu, masu dafa abinci, ma’aikatan gida, manajoji, da kowa da kowa za su samu damar mallakar wani kaso na wannan dama.

Dangote ya kara da cewa an tsara wannan damar ne domin masu sayan hannun jari su yi tanadin gaba ta hanyar zuba wannan jari.

Dangote ya bayyana tsarin a matsayin “IPO na jama’a”.

Za a kaddamar da IPO din a ranar 14 ga Satumba. Zai samar da riba mai yawan da ake sa ran kasashen waje za su zuba a Najeriya, bayan da FTSE Russel ta mayar da kasar zuwa matsayin kasuwar ta kan gaba. Wannan matsayi ya dawo ne bayan kusan shekaru 3 da kasar ta yi a kasa ba tare da rarraba tsarin ba, wanda hakan ya hana masu zuba jari na kasa da kasa shigowa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here