Zaben 2027: Za a dauki mataki kan duk wanda ya aikata ba daidai ba – Shugaban INEC ya gargadi jami’ai

Joash Amupitan INEC (1)

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya gargadi jami’an zabe cewa za a dauki mataki kan duk wanda ya aikata ba daidai ba, inda ya bukaci su kasance ‘yan babu ruwana su kuma gudanar da aikinsu cikin amana a yayin babban zaben 2027.

Amupitan, ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin a Legas yayin Taron Tattaunawa na Yankin Kudu masoYamma da ma’aikata kan shirye-shiryen hukumar na zaben 2027.

Ya ce ba za a lamunci nuna goyon baya ga jam’iyya, sakaci wajen gudanarwa, ko cin hanci da rashawa ba tare da jaddada cewa kare mutuncin tsarin zabe ba abin sayarwa ba ne.

“Ina so na bayyana a fili cewa nuna goyon bayan jam’iyya, sakaci a bangaren gudanarwa, ko cin hanci da rashawa ba za mu lamunce su ba.

Za mu tilasta dokokin mu na gudanarwa, kuma kowane jami’i dole ne ya fahimci cewa kare mutuncin hukumar INEC ya fi karfin a sayar da shi,” in ji shi.

Shugaban INEC ya bukaci jami’an zabe da su gudanar da zabe ba tare da nuna fifiko ga wani dan takara ko jam’iyya ba.

Ya ce Dokar Zabe ta kara jaddada bukatar zama dan babu ruwana ga ma’aikatan da ke cikin zabe.

“Tambayar ba zata kasance ‘Wane ne zai amfana da wannan mataki?’ Kamata ya yi ta zama ‘Me doka ta bukaci in yi?’ Wannan ita ce tarbiya da ke kare tsarin zabe da kuma jami’in zabe,” in ji shi.

Amupitan ya kuma gargadi jami’ai da kada su yi kokarin samar da mafita da kansu a inda doka ko jagororin hukumar suka tsara hanyar da za a bi.

“Daya daga cikin matsalolin da ke tasowa a tsari shi ne sha’awar warware matsaloli ta hanyoyin da ba na hukuma ba.

“A tsarin gudanar da zabe, wannan mataki na iya zama mai hatsari. Inda doka ta samar da hanya, ku bi ta. Inda hukumar ta bayar da jagoranci ko umarni, ku bi shi. Idan matsala ta taso, ku kai ta ta hanyar da ta dace a cikin tsari,” in ji shi.

Ya ce nasarar zaben 2027 za ta dogara ne da yadda jami’an zabe za su bi doka.

“Dokar Zabe da aka rubuta da kyau ba za ta iya tabbatar da zabe na gaskiya ita kadai ba. Fasahar zabe mai ci gaba ba za ta iya tabbatar da amana ita kadai ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ba za ta iya tabbatar da amincewar jama’a ita kadai ba. Amincewar zabe ta dogara ne kan yadda jami’an da aka dorawa nauyi za su bi doka,” in ji Amupitan.

Ya bukaci ma’aikata su da su san doka, su fahimci nauyin dake kansu, su kasance ‘yan babu ruwana, su rubuta duk abin da suka yi, su kuma kare mutuncin tsarin zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here