Hukumar Rajistar Malamai ta Kasa (TRCN) ta gargadi malamai, masu makarantu da masu neman rajista da kada su fada komar shafukan bogi na zamba da kuma mutanen da ke ayyana kansu a matsayin wakilan hukumar.
Shugabar Hukumar ta TRCN, Dr Ronke Soyombo, ce ta yi wannan gargadin a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, biyo bayan rahotanni kan wasu mutane da kungiyoyi da ake zargi da amfani da sunan hukumar da kuma shaidarta wajen damfarar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Soyombo ta bayyana cewa TRCN ba ta ba wa wani wakili, mai ba da shawara, wani mutum, ko ma’aikaci iko ya karbi kudi ko ya gudanar da rajista, ba da takardar shaida, lasisi, daukar aiki, ko karin girma ba ta hanyoyin da aka amince da su ba na hukumar.
Ta kara da cewa shafin intanet na hukumar www.trcn.gov.ng, shi kadai ne halartaccen shafin da aka amince da shi don samun bayanai kan shirye-shiryen da ayyukanta.
“Hukumar ba ta da wani shafi, kuma bata amfani da wani shafi rajista in ban da shafinmu na hukuma www.trcn.gov.ng,” in ji ta.
Ta bukaci malamai da sauran masu ruwa da tsaki da su kiyayi rubuce-rubucen kafofin sada zumunta, sakonnin WhatsApp, imel da kuma shafukan yanar gizo da ke cewa suna bayar da damar yin rajistar TRCN, Jarabawar Kwarewa ta (PQE), takaddun shaida da sauran ayyuka.
Haka ta kuma gargadi jama’a da kada su rika tura kudi zuwa asusun banki na mutane, inda ta jaddada cewa hukumar ba ta karbar kudade ta irin wadannan hanyoyi.
A cewarta, takaddun shaida da lasisin da aka gudanar ta hanyoyin da ba na hukuma ba, hukumar za ta ayyana su a matsayin marasa amfani.












































