Dakarun rundunar ta 12 Brigade, karkashin Division ta 2 ta Sojin Najeriya, hadin gwiwar Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), mafarauta na gida da mambobin Kungiyar ‘Yan Banga, sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi.
An ceto wadanda aka yi garkuwar da su ne a ranar Litinin, 31 ga Agusta, 2026, yayin wani samamen ceto da aka gudanar a yankin dazuzzukan Egume da Ochaja na jihar.
Sojojin sun ce samamen ya biyo bayan garkuwa da fasinjoji da yawa a kan hanyar Alloma, Ejule da Itobe.
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa, Leftan Hassan Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce jami’an hadin gwiwar sun kaddamar da samamen ne bayan sun sami sahihan bayanai kan inda wadanda aka sacen suke.
A cewarsa, sojojin Brigade ta 12 da jami’an sauran hukumomin tsaro na hadin gwiwa, tare da mafarauta da ‘yan banga daga Karamar Hukumar Dekina, sun taso ne daga Hedikwatar Bataliya ta 21 inda suka fara tsananta binciken hadin gwiwa a dazuzzukan da ke kewaye da yankin.
Ya bayyana cewa samamen ya kai ga nasarar ceto dukkan mutane 21 da aka sace, wadanda suka kunshi maza takwas da mata 13, daga yankin dazuzzukan na Egume da Ochaja.
Sai dai, Abdullahi ya ce daya daga cikin mazan da aka ceton ya sami raunin harbin bindiga a kafa yayin faruwar lamarin.
Ya ce an kai wanda abin ya shafa cikin gaggawa zuwa dakin asibitin Bataliya ta 21 don ba shi kulawar likita.
“Wadanda aka ceton a halin yanzu suna samun kulawa a Hedikwatar Bataliya ta 21, yayin da ake daukar kwararan matakai don ganin an sada su lafiya da iyalansu da kuma hukumomin da suka dace,” in ji shi.
Kwamandan Brigade ta 12 na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya jinjina wa sojojin da sauran jami’an tsaron da suka shiga samamen saboda jarumtarsu, jajircewarsu, da kuma kyakkyawan hadin gwiwar da suka nuna, wanda ya ce shi ne ya taimaka wajen samun nasarar ceton.
Ya tabbatar wa mazauna yankin da matafiya cewa rundunar, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, za su ci gaba da gudanar da samamen bincike da ceto domin kare rayuka da inganta tsaro a yankunansu.
Haka kuma, rundunar sojin ta yi kira ga jam’a da su kasance masu sanya ido, sannan su rika ba hukumomin tsaro sahihan bayanai akan lokaci domin tallafa wa kokarin yaki da garkuwa da mutane da sauran laifuka.












































