Al-Qa’ida ta sanar da mutuwar shugabanta a Yemen

Khalid Batarf, Al-Qa'ida, mutuwar, Yemen
Reshen Al-Qa'ida na ƙasar Yemen ya sanar da mutuwar shugabansa, a wani yanayi da ba'a fayyace ba. A wani bidiyon da aka wallafa a shafin yanar gizo da...

Reshen Al-Qa’ida na ƙasar Yemen ya sanar da mutuwar shugabansa, a wani yanayi da ba’a fayyace ba.

A wani bidiyon da aka wallafa a shafin yanar gizo da ƙungiyar a yankin Larabawa ta AQAP ta yi, ya nuna gawar Khalid Batarfi an yi mata sutura an ajiye a gaban tutar ƙungiyar.

A wata sanarwa da wani ƙusa a ƙungiyar ya karanta, ba’a bayyana musabbabin mutuwarsa ba, sai dai ta yi amfani da kalmar cewa Allah ne ya karɓi ransa, abin da ke nuna cewa ba kashe shi aka yi ba kamar wanda ya gabace shi.

Karin labari: Ramadan: Sanata Barau ya yiwa Kasa addu’a tare da shirin tallafawa mabukata

Batarfi, ɗan asalin Saudi Arabia na cikin shekarunsa na 40 a lokacin da ya karɓi jagorancin AQAP a shekarar 2020.

Amurka ta ayyana shi a matsayin ɗan ta’adda a shekarar 2018 kuma ta sanya kuɗi dalar Amurka miliyan biyar a kansa.

Jami’in AQAP wanda ya karanta sanarwar, Abu Khubaib al-Sudani ya sanar da cewa majalisar shura ta ƙungiyar ta zaɓi Saad bin Atef al-Awlaki a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.

Karin labari: Ramadan: ‘Yan kasuwa a jihar Kano sun koka kan karancin ciniki

An taɓa ɗaukar AQAP a matsayin reshe mafi ƙarfi da tasiri kuma mafi hatsari na ƙungiyar al-Qa’ida.

AQAP ta kai munanan hare-hare a cikin Yemen da kuma Saudi Arabia da kuma yunkurin kai wani harin bam kan jirgin saman Amurka, harin da aka daƙile.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here