Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan PFIPC da ake cece-kuce a kai, ya umarci Sufeto Janar na ‘yan Sandan Kasa, Olatunji Disu, da ya gabatar da wanda ya yi ikirarin cewa shi ne Babban Daraktan hukumar, Adeyemi Adeniyi, a gaban kwamitin a ranar Laraba.
An ba da wannan umarni ne a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da sauraron sakamakon binciken da aka yi a Ginin Majalisar Dokoki ta Kasa, Abuja.
An umarci Mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda, Bashir Abdullahi wanda ya wakilci Sufeton a gaban kwamitin da ya tabbatar Adeyemi ya bayyana da rana a ranar Laraba domin ya taimakawa ‘yan majalisa wajen ci gaba da binciken ayyukan hukumar.
Kwamitin yana binciken yadda PFIPC, duk da cewa ba a kafa ta bisa doka ba, ta samu ofis a hawa na uku na Ginin Sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja kuma aka ware mata kusan Naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kudin 2026.
Umarnin ya biyo bayan tabbatar da jami’an ‘yan Sanda suka yi na wasu muhimman sassan binciken laifuka, ciki har da wasikun da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ya aike yana zargin Adeyemi da yin zamba ta hanyar bayyana kansa a matsayin Babban Daraktan PEAC da kuma PFIPC.
Shugaban Kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce lallai ne Adeyemi ya bayyana saboda tsananin zargin da aka yi da kuma manyan hukumomin da abin ya shafa.
“Wannan kwamitin lallai yana bukatar wanda ake zargi da ya bayyana. Ya shafi sunan mutane, daraja, sunan hukumomi da darajar hukumomin.
“Ba zabi ba ne a yanzu, muna bukatar shi a nan domin ya tabbatar mana da wasu takardu ta yadda ba za mu lalata binciken mu ba domin mu mika rahoton mu a kan lokaci,” in ji Gagdi.
Daga nan kwamitin ya umurci Sakatarensa da ya aika da sanarwar hukunci zuwa ga Sufeton Janar na ‘yan Sanda.
“Kwamitin ya yanke hukuncin cewa Sufeton Janar na ‘yan Sandan Tarayyar Najeriya ya gabatar da Mista Adeyemi ranar Laraba da rana. Wannan shi ne hukuncin kwamitin,” in ji Gagdi.













































