A yau Litinin ne jam’iyyar APC sanar da dakatar da babban taronta na kasa, wanda aka shirya gudanarwa tun a ranar 26 ga watan Fabrairu har sai zuwa wani lokaci.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan Litinin 21 ga watan Fabrairu, 2022 mai dauke da sa hannun shugaban riko na jam’iyyar, Gwamna Mai Mala Buni da sakataren riko, Sanata John Akpanudoedehe, wadda aka aikewa shugaban hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Jam’iyyar ta kara da cewa za a gudanar da zabukan shiyyar ne a ranar 26 ga Maris, 2022 yayin da ake sa ran INEC za ta turo jami’anta don sanya ido kan aikin.













































