Ronaldo ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya ci kwallo a gasar cin Kofin Duniya shida daban-daban

Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa na farko da ya ci kwallo a gasar cin Kofin Duniya shida daban-daban a ranar Talata, bayan da ya ci kwallaye biyu bayan Portugal ta yi masara da ci 5-0 a kan Uzbekistan.

Ronaldo mai shekaru 41 ya kafa tarihin a minti na 6 lokacin da João Cancelo ya tsallafa masa da kwallon. Bayan minti na 39, ya sake zura kwallo bayan da Bruno Fernandes ya tallafa masa da kwallon.

An ba Ronaldo kyautar “Dan wasan da ya fi kowa kwazo” a wasan.

Wadannan kwallaye sun sa shi ya zama dan wasa na biyu mafi tsufa da ya ci kwallo a gasar cin Kofin Duniya bayan Roger Milla na Kamaru, wanda ke da shekaru 42 lokacin da ya ci kwallo a gasar 1994 a Amurka.

Kwallayen Ronaldo sun zo ne bayan ya sha soku bisa gaza ci kwallo a wasan farko da Portugal ta buga Congo in da suka tashi 1-1.

Ronaldo da kyaftin din Argentina Lionel Messi sun zama ‘yan wasa maza biyu tilo a tarihi da suka buga gasar ta Kofin Duniya sau shida a wannan shekara.

Ya fara zura kwallon tun wasansa na farko a 2006, kuma ya ci kwallaye a 2010, 2014, 2018 da 2022.

Kwallayen da Ronaldo ya ci a ranar Talata sun kai adadin kwallayensa 10 a gasar baki daya. Messi na da kwallaye 18 bayan ya ci 3 a wasan farko na Argentina da Aljeriya, sannan ya kara ci kwallaye biyu a ranar Litinin da Austria wanda ya sa shi ya zama dan wasan da ya fi kowa ci kwallo a tarihin gasar.

Wannan na iya zama Kofin Duniya na karshe ga Ronaldo, wanda ya lashe Kofin Turai tare da Portugal a 2016 kuma ya lashe Gasar Zakarun Turai sau 5 tare da Manchester United da Real Madrid.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here