Najeriya ta Doke ƙasar Benin a wasan neman samun tikitin zuwa gasar cin kofin Duniya da ake fafatawa a yanzu haka.
Nigeria dai ta doke kasar ta Benin da ci 4-0 a wasan da aka fafata a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyon jihar Akwa Ibon.
Dan wasa Victor Osimhen ne dai ya zura kwallaye uku a wasan inda ya zura ƙwallaye biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci bayan an dawo kuma ba jimawa ya zura ƙwallo ta uku.
Bayan cikar lokacin wasan inda aka kara mintuna 5 dan wasa F. Onyeka ya zura kwallo ta 4 a mintuna 91.
Yanzu dai Najeriya ta ƙare a matsayin ta 2 da maki 17 a rukunin da take na C inda kasar Afrika ta Kudu ta kare a matsayin ta 1 da maki 18, sai kasar Benin da ta ƙare a matsayin ta 3 itama da maki 17 wanda tazarar ƙwallayen ta baiwa Najeriya damar tsayawa a matsayin ta 2.
Kasar Afrika ta Kudu dai ta doke Rwanda daci 3 babu ko ɗaya a wasan da suka fafata su ma.













































