Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara wani asibiti a Jigawa

A JIG
A JIG

Daga Moses Akoji

Bayan rahoton da Jaridar Solacebase ta yi an gyara asibitin garin Bardo dake karamar hukumar Taura a Jigawa.

Samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ya kasance gaba-gaba cikin manufofin gwamnatin jihar Jigawa.

Sai dai duk da haka kananan asibitoci a fadin jihar na cikin wani hali tsawon shekaru, duk da kiraye-kirayen da ake yi na kara zuba jari a fannin kiwon lafiya a matakin farko.

A JIG 1, Rahoton
Kafin a Gyara Asibitin

Jaridar Solacebase ta kawo sauyi a harkar kiwon lafiya a fadin jihar Jigawa, a cikin wannan rahoto, Aliyu Mansur ya rubuta kokarin gwamnati na farfado da lalataccen asibitin Bardo da aka yi watsi da shi tsawon shekaru.

Karanta wannan: Badakalar N37bn: EFCC Ta Gayyaci Tsohuwar Ministar Buhari

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Jigawa bayan rahoton jaridar ta Solacebase ta gyara asibitin Bardo dake cikin wani hali sama da shekaru 7.

A JIG 2
Bayan an gyara Asibitin

Gyaran asibitin ya zo ne bayan rahoton Jaridar Solacebase da kuma wayar da kan al’ummar Bardo da kungiyar masu wallafa jaridu na Internet ta yi musu akan yadda za su yi korafi tare da nuna rashin jin dadinsu game da yadda aka yi watsi da asibitin su.

Gaskiyar magana dai ita ce, al’ummar Bardo dake karamar hukumar Taura, suna da adadin mutane fiye da dubu arba’in (40,000), kuma duk da yawan su karamin asibiti daya ne kawai da su, shima ya lalace, sannan babu isassun masu kula da lafiyar al’ummar yankin.

A duk lokacin da rashin lafiya ko nakuda ta tasowa wasu a yankin sai sun yi tafiya mai nisan gaske kafin riskar wani asibitin, ga kuma matsalar rashin kyawun hanya da suke fuskanta.

A JIG 2, rahoton
Bayan an gyara asibitin

Gyaran asibitin ya zo ne a matsayin cika fata ga al’ummar yankin Bardo ganin yadda tsohon asibitin na su ya zama abin sha’awa sakamakon gyaran da aka yi masa.

A wata ziyara da Jaridar Solacebase ta kai asibitin wanda aka yi watsi da shi a baya yanzu haka an yi masa gyare-gyare.

Sale Lawal, shi ne shugaban asibitin ya bayyana farin ciki bisa gyaran da aka yi musu, inda ya yi fatan samar da kayayyakin aiki da kuma kara yawan ma’aikata don inganta harkokin kiwon lafiya a yankin.

A nasa bangaren sabon dagacin Bardo, Tijjani Usman, ya yabawa kokarin jaridar Solacebase tare da bayyana hakan a matsayin kishin kasa.

Karanta wannan: Ya Zama Wajibi A Hukunta Wike – Dan Takarar Gwamna Ya Gayawa PDP

Dakta Kabir Ibrahim Aliyu, shi ne babban sakataren hukumar lafiya a matakin farko na jihar, a wata hira da manema labarai, ya shaidawa Jaridar Solacebase cewa yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci farfado da asibitoci ta hanyar yi musu gini mai inganci tare da zuba kayan aiki na zamani a fadin jihar.

Aliyu ya ce daya daga cikin manyan abubuwan da hukumar ta sa gaba shi ne bayar da tallafi ga ma’aikatan asibitocin jihar domin saukaka musu ayyukan su.

Ya kara da cewa, bayan farfado da asibitocin, hukumar tana aiki da masu ruwa da tsaki domin duba yadda za’a taimaki tsarin kiwon lafiya a fadin jihar.

Ya bayyana cewa samar da isassun kayan aiki da magunguna da wutar lantarki da ruwa mai tsafta a asibitocin zai taimaka matuka wajen inganta harkokin kiwon lafiya a jihar.

A JIG 3
Al’ummar Yankin lokacin da Jaridar solacebas ta ziyarce su

Ya jaddada bukatar inganta tsarin kananan asibitoci a jihar, inda yace gwamnatin jihar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya asibitocin.

Karanta wannan: Majalisar Wakilai ta bada shawarar hukunta wadanda basa biyan ma’aikata Albashi

Mazauna yankin na Bardo, sun yi kira ga gwamnati da ta ba da fifiko ga harkokin kiwon lafiyar mazauna yankunan karkara.

A JIG 4

Jaridar Solacebase ta wallafa wannan rahoto ne da taimakon cibiyar gudanar da binciken kwakwaf a aikin Jarida ta Wole Soyinka da hadin gwiwar Media Engagement for Development, Inclusion, and Accountability Project (CMEDIA) da kuma tallafin Gidauniyar MacArthur.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here