Majalisar Wakilai ta bada shawarar hukunta wadanda basa biyan ma’aikata Albashi

Reps
Reps

Majalisar Wakilai ta gabatar da kudirin dokar hukunta kamfanoni da ma’aikatun da basa biyan ma’aikata albashi a fadin kasar nan.

Idan aka aiwatar da dokar, ma’aikata na iya bukatar a biya su hakkin su ta hanyar rubutun wasikar neman hakki.

Kudurin wanda dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Agege a jihar Legas, Wale Hammed ya gabatar mai taken “Kudirin kare hakkin ma’aikata na 2023, ya tsallake karatu na farko.

Karanta wannan: Sojin Isra’ila sun bayyana cewa suna gwabza kazamin fada a kudancin Gaza

Sashe na 7 (1 cikin baka) ya tanadi cewa bai halatta ga kowane ma’aikaci ya “Ki ko ya yi sakaci wajen biyan albashin ma’aikatansa ba.”

Section 8 (1) of the bill states that if an employee’s compensation remains unpaid beyond the specified period permitted by this legislation, the employee may submit a written demand to their employer for the payment of their entitlement if they wish to assert their claim.

Sashe na 8 (1 cikin baka) yace idan har aka gaza biyan ma’aikaci hakkin sa har tsawon wani lokaci, dokar ta bawa ma’aikaci izini ya gabatar da bukatarsa a rubuce ga wanda yake yi wa aiki domin ya biya shi hakkinsa.

A cewar kudirin dokar, wadanda aka samu da laifin kin biyan ma’aikatansu albashi za su fuskanci daurin wata uku zuwa shida a gidan yari, ba tare da yuwuwar biyan tara ba.

Hakazalika, kamfanin da ya ki bin umarnin kotu game da biyan albashin ma’aikatansa, zai iya fuskantar tarar Naira dubu 10 a kullum, ko kuma “A rufe shi har tsawon wata uku.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here