Kotu ta bukaci FAAN da mazauna gidajen ma’aikatan jiragen sama a Kano su tattauna sulhu kan takaddamar mallakar gidaje

FAAN Logo

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a ranar Alhamis ta bukaci Hukumar Kula da Filayen Jirgen Sama ta Najeriya (FAAN) da mazauna Rukunin Gidajen Ma’aikatan Jiragen Sama da su yi kokarin warware takaddamar da ta dade kan mallakar gidajen gwamnati ta hanyar sulhu.

SolaceBase ta ruwaito cewa Mai Shari’a Simon Amobeda ne ya ba da wannan shawarar bayan zaman kotun kan karar da Kwamitin Amintattun Kungiyar Mazauna Rukunin Gidajen da wasu mutane shida suka shigar, inda ya ce sulhu na iya samar da mafita mai dorewa ga rikicin.

Alkalin ya kuma ba da umarnin cewa dukkan bangarorin su dakata da daukar kowani mataki a yanzu har sai an yanke hukunci kan bukatun da ke gaban kotu.

Mazauna gidajen na kalubalantar abin da suka bayyana a matsayin yunkurin FAAN na korarsu daga gidajen da suke cewa sun saye su bisa doka karkashin shirin Monetization Programme na Gwamnatin Tarayya.

Takardun kotu sun nuna cewa masu kara suna neman umarnin kotu na hana Ministan Harkokin Jirgi da Sufurin Sama, FAAN, Sakataren Gwamnatin Tarayya da Sakataren Kwamitin Shugaban Kasa na Aiwatar da Haya/Sayar da Kadarorin Gwamnati daga tsoratarwa, tsangwama ko korar su daga cikin gidajen.

Haka kuma suna neman kotu ta ba da umarnin a sakin albashi da kudaden fansho da ake zargin an rike na wasu daga cikin ma’aikata da masu ritaya da lamarin ya shafa, har sai an yanke hukunci kan babbar kara.

A zaman na Alhamis, Lauyan FAAN, Olukayode Makinde, ya sanar da kotu cewa hukumar ta shigar da bukatar neman karin lokaci domin daidaita takardunsu, yana mai cewa bukatar da masu kara suka shigar ba ta isa a saurara ba tukuna.

Lauyan masu kara, Amos Ibrahim Ango, bai yi hamayya da wannan bukatar ba, sai Mai Shari’a Amobeda ya amince da ita.

Lauyan da ke wakiltar wanda ake kara na uku da na hudu, Ishaku Inusa Mato, ya shaida wa kotun cewa su ma waddanda yake wakilta sun shigar da nasu hujjojin bayan an mika musu takardun karar.
Masu kara sun kara zargin cewa jami’an Tsaron Filayen Jirgi (AVSEC) na ci gaba da tsoratar da mazauna gidajen duk da cewa karar na gaban kotu.

Da yake magana a madadin masu kara, Sakataren Kungiyar Mazauna Rukunin Gidajen, Obadaki Muhammad Mustapha, ya bukaci kotu da ta ba Sakataren Gwamnatin Tarayya dama ya jagoranci kokarin sulhu, yana mai cewa yana da kwarin gwiwar cewa ofishin zai tabbatar da adalci ga dukkan bangarori.

Mai Shari’a Amobeda ya baiwa bangarorin biyu shawarar su yi la’akari da warware rikicin ta hanyar sulhu da gaskiya, yana mai cewa sulhu mai aminci zai yi wa samar da adalci.

Koyaya, ya gargadi dukkan bangarorin da su guji yin wani abu da zai yi illa ga halin da ake ciki a yanzu har sai an saurari bukatun da ke gaban kotu.

An dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga watan Oktoba, 2026, domin ko dai a ji rahoton sakamakon kokarin sulhu ko kuma a saurari bukatun da ke gaban kotu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here