Mai rikon shugabancin jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Etteh Ibas (mai ritaya), ya yi kira ga kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) da ta mayar da Naira miliyan 300 da gwamnatinsa ta biya domin karbar bakuncin babban taron shekara-shekara na 2025.
A baya dai kungiyar ta NBA ta janye matakin da ta dauka na gudanar da taron a jihar Rivers, bisa dalilinta na cewa an kafa dokar ta baci da kuma rugujewar tsarin dimokuradiyya a jihar a matsayin dalilan da suka sa aka mayar da taron zuwa Enugu.
Dangane da wannan ci gaban a ranar Litinin, Ibas ya bayyana cewa, “Duk da cewa muna mutunta ‘yancin NBA na zabar wuraren da za ta yi taronta, amma mun ga cewa kungiyar duk da matsayin ta ba ta yi magana game da maido da Naira miliyan 300 da gwamnatin jihar Rivers ta riga ta biya don samun damar karbar bakuncin taron na 2025 ba.”
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Hector Igbikiowubo, babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga gwamnatin jihar Rivers, a ranar Litinin.
Ya kara da cewa, “Idan da gaske NBA ta tsaya kan ka’ida, ya kamata ta nuna mutuncin ta ta hanyar dawo da wadannan kudade cikin gaggawa maimakon cin gajiyar jihar da a yanzu take bata sunan jama’a.”