Tsohon Babban Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya fice daga jam’iyyar APC.
Adamu dan takara ne a zaben fidda gwanin gwamnan APC da aka kammala a jihar Nasarawa.
Tsohon IGP ya fice daga APC ne a ranar Litinin, a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar na Karamar Hukumar Makama da ke Karamar Hukumar Lafia ta jihar.
“Yau na aika muku wasika, ga shugabannin jam’iyya na mazabata, musamman shugaba, kan shawarata ta ficewa daga APC nan take.
“Yanke irin wannan shawara ba ta da sauki; duk da haka, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a cikin jam’iyyar, musamman yadda aka gudanar da zaben fidda gwanin gwamna a jihar, sun sa ya zama mai wahala in ci gaba da ayyukan siyasata a karkashin APC,” in ji shi.
Ya yi korafin rashin gudanar da dimokuradiyya ta cikin gida, adalci, gaskiya daidaiton bada dama ga ‘yan takara a lokacin zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar.
“Na yi imani sosai cewa dimokuradiyya ta cikin gida, adalci, gaskiya daidaiton bada dama ga ‘yan takara da mambobi ya kamata su jagoranci harkokin kowace jam’iyyar siyasa a tsarin irin na dimokuradiyya.
“Abin takaici, abubuwan da suka faru a dab da zaben fidda gwanin ba su bi wannan ka’ida ba, lamarin da ya sa na rasa amincewa da shugabancin jam’iyyar a jihar.
“Bayan tattaunawa da magoya bayana, abokan siyasa da iyalina, na yanke shawarar barin jam’iyyar APC don cimma muradina na siyasa a wata jam’iyyar daban.
“Da fatan za ku karbi wannan wasika a matsayin ta barina jam’iyyar,” in ji shi.
Adamu ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na yin hidima da bayar da gudummawa ga ci gabanta yayin da yake memba.
Ya kuma gode wa mambobin APC a matakai daban-daban bisa hadin kai da goyon bayan da suka ba shi yayin da yake memba.












































