Cikin Hotuna: Ganduje ya karbi bakuncin Kawu Sumaila, Rurum, Baffa Bichi, Sha’aban Sharada, Diggol a matsayin sabbin ‘yan APC

WhatsApp Image 2025 04 24 at 19.28.10 750x430

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi wasu fitattun jagororin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da dama da suka koma APC.

SolaceBase ta ruwaito daga cikin wadanda suka koma zuwa jam’iyyar akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar mazabar Kano ta Kudu; Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rano/Kibiya/Bunkure, Dr. Baffa Bichi, tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, da Hon. Badamasi Ayuba, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Danbatta/Makoda.

Sauran sun hada da Hon. Abdullahi Sani Rogo, Rt. Hon. Zubairu Hamza Masu, Hon. Muhammad Diggol, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, da Hon. Abbas Sani Abbas.

WhatsApp Image 2025 04 24 at 19.28.11 768x512

Da yake jawabi bayan wata ganawar sirri da sabbin masu shiga jam’iyyar Ganduje ya ce, “A APC, mun yi imani da shugabanmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mun yi imani da sake fasalin tattalin arzikinsa, mun yi imani da ajandarsa ta “Renewed Hope” kuma wani bangare na sabunta fata na siyasa yana kokarin zage damtse don samun karin mabiya a jam’iyyar.

WhatsApp Image 2025 04 24 at 19.28.12 1 768x512

WhatsApp Image 2025 04 24 at 19.28.13 768x512WhatsApp Image 2025 04 24 at 19.28.12 768x512

“Mun fara ne da zaben gwamnoni ta hanyar dimokuradiyya, musamman a jihar Edo, wanda yake PDP, muka zabe, muka yi nasarar cin zabe, yanzu yana APC.

Labari mai alaƙa: Sanata Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC

Ba na so in tona asirin mu, amma abin da nake gaya muku shi ne, a APC, 2027 an gama aiki.”

A nasa bangaren, Sanata Kawu, wanda ya jagoranci tawagar ya ce, “Wannan shi ne haduwar masu tunani iri daya a NNPP jihar Kano.

A lokuta da dama dai masu sauya shekar sun bayyana rashin gamsuwarsu a bainar jama’a dangane da abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci da kuma bata gari a cikin jam’iyyar NNPP, wanda ake zargin shugaban jam’iyyar, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya shirya shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here