DG na PGF ya musanta cire Uzodimma a matsayin shugaban gwamnonin APC

Hope Uzodimma new 750x430

Darakta-Janar na Progressive Governors Forum (PGF), Folorunsho Aluko, ya karyata rahotannin da ke cewa an cire Hope Uzodimma a matsayin shugaban kungiyar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Juma’a, Aluko ya ce ba a yanke irin wannan hukunci ba, yana mai jaddada cewa ba a gudanar da wani taro na kungiyar ba domin wannan batu.

“Ba a gudanar da wani taro na kungiyar ba inda aka yanke irin wannan hukunci. Sakateriyar PGF ba ta da wani rikodin, kuma ba ta da masaniya game da wani kuduri na cire shugabanta,” in ji shi.

Ya sake tabbatar da matsayin Uzodimma, yana mai cewa Gwamnan Jihar Imo na nan daram a kan jagorancin kungiyar.

“Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, shi ne har yanzu shugaban Progressive Governors Forum,” in ji Aluko.

DG na PGF ya kuma bayyana cewa akwai hadin kai a cikin kungiyar, yana mai cewa “kungiyar kanta a hade yake, kuma mai jajircewa wajen gudanar da ayyukansa.”

Wannan musantawar ta biyo bayan wani rahoto da Arise News ta fitar a daren Alhamis da ke cewa kusan gwamnonin 20 sun hadu a Ogun State Governor’s Lodge da ke Abuja, inda ake zargin an yanke hukuncin cire Uzodimma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here