Flying Eagles da Golden Eaglets sun samu sabbin kociyoyi

NFF

Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) ta nada Abdu Maikaba da Eboboritse Uwejamomere a matsayin manyan kociyoyin kungiyoyin kwallon kafa na ‘yan kasa da shekaru 20 da 17.

A cikin wata sanarwa da Ademola Olajire, Daraktan Sadarwar hukumar ta NFF ya fitar, ya ce kwamitin zartarwar hukumar ya amince da shawarar kwamitin Kwararru da Ci gaba da nada sabbin kociyoyin biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Maikaba ya taba koyar da Golden Eaglets, sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin kocin Flying Eagles a lokacin Paul Aigbogun.

Ya kuma rike manyan kungiyoyi ciki har da Enyimba, Wikki Tourists, Kano Pillars da Plateau United a lokacin da yake aiki a matsayin koci.

Maikaba ya kuma jagoranci Akwa United zuwa nasara a gasar Federation Cup ta 2017, wadda ita ce gasar kwallon kafa ta cikin gida mafi dadewa a Najeriya.

NAN ta kuma ruwaito cewa Uwejamomere ya zama babban kocin Golden Eaglets bayan ya yi shekaru da yawa a matsayin mai nazari da Super Eagles da Super Falcons.

A yanzu haka shi ne shugaban makarantar kwallo ta Sporting Lagos FC, wadda kwanan nan aka ta samu damar shigowa gasar Nigeria Premier Football League (NPFL).

Uwejamomere ya kuma yi aiki a matsayin kocin ci gaban matasa a Millwall FC, Gillingham FC da Nottingham Forest FC a Ingila.

A baya ya taba zama babban kocin Stormers FC da ke Abeokuta. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here