Za a sake buɗe gidan adana kayan tarihin Jamus watanni 5 bayan an sace gwal

German museum reopens 5 months after gold treasure theft
German museum reopens 5 months after gold treasure theft

Za a sake buɗe gidan adana kayan tarihin Jamus watanni biyar bayan wata gagarumar satar wani katafaren zinare na Celtic da ake ajiye da shi a wurin.

Za a buɗe gidan kayan tarihi na Celtic Roman da ke Manching a Bavaria daga 2 ga Mayu, kamar yadda gidan kayan gargajiya da adana t kayan tarihi na Jiha ya sanar a cikin wata sanarwa a yau Juma’a.

Sai dai kuma za a ci gaba da rufe ɓangaren da a ka fasa aka kwashe gwala-gwalan a watan Nuwamba 2022.

Sai an tattauna yadda za a ci gaba da amfani da sashen nan gaba,” in ji sanarwar.

A daren ranar 22 ga watan Nuwamba ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai harin, inda su ka kutsa cikin gidan adana kayan tarihi na Manching da ke da nisan kilomita 75 daga arewacin Munich, su ka sace wata taska ta tsabar zinare guda 483 na Celtic na miliyoyin kuɗi.

An kiyasta kimar kayan gwal din mai nauyin kilogiram 3.7 a kusan dala miliyan 275, amma karancin sulallanna tarihi ya sanya kimarsu ta hakika a cikin miliyoyin.

Ofishin ƴan sandan jihar Bavariya masu binciken laifuka ne ke binciken laifin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here