Kano: Jigo a APC Hamza Darma ya rasu yana da shekaru 76

IMG 20260821 WA0388 750x430

Fitaccen dan jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Hamza Usman Darma, ya rasu yana da shekaru 76.

SolaceBase ta ruwaito cewa Alhaji Hamza Darma ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a ranar Juma’a.

A cewar majiyoyi daga cikin iyalansa, za a gudanar da jana’izar sa a gidansa da ke Hororo, kusa da Jami’ar Maryam Abacha ta Najeriya (MAAUN) a yau.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here