An gano gawarwaki 46, an ceto mutane 15 a hatsarin jirgin ruwa a Sokoto

154 feared dead in Kebbi boat mishap

An gano gawarwaki 46 yayin da aka ceto mutane 15 da rai bayan hatsarin jirgin ruwa da ya auku a garin Gorau, Karamar Hukumar Goronyo ta Jihar Sokoto.

An ce jirgin na dauke da fasinjoji 77 ciki har da manoma, mata da yara, wanda ya kife da sassafe a ranar Alhamis jim kadan bayan ya tashi daga cikin garin.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Sokoto, DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce har zuwa lokacin da suke fitar da wannan labari, tawagar ceto na ci gaba da binciken fasinjoji 16 da ba a san inda suke ba.

Ya ce aikin bincike da ceto ya hada masu ruwa na gida, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ’Yan Sanda.

“An gano gawarwaki 46 zuwa yanzu, yayin da aka ceto mutane 15 da rai. Tawagar ceto da ta kunshi masu ruwa na gida, NEMA, SEMA da ’Yan Sanda na ci gaba da binciken sauran mutane 16,” in ji Rufai.

Ya kara da cewa “mutane 77 ne ke cikin jirgin a lokacin da hatsarin ya faru.”

Wannan bala’in ya jefa garin Gorau cikin bakin ciki, yayin da iyalai ke jira da damuwa don jin labarin ’yan uwansu da har yanzu ba a samu ba.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce hatsarin ya faru da safiyar Alhamis yayin da fasinjojin ke tafiya gonakinsu.

Ya ce masu ruwa na gida nan take suka shiga aikin ceto, inda aka gano gawarwaki da yawa daga cikin ruwa

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here