Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) da ke Jihar Jigawa, ta musanta zargin keta hakkiin daukar ma’aikata, bata suna da kuma hana damar kare kai da tsohuwar malamar jami’ar, Dr. Ramla Muhammad Kamal, ta yi biyo bayan korar ta da aka yi daga aiki.
A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Directan Yada Labarai na Jami’ar, Abdullahi Yahaya Bello, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, ta bayyana cewa korar ta biyo bayan tsarin gudanarwa da na horon doka, kuma yana da alaka da gazawar Dr. Kamal na komawa bakin aiki bayan ta kammala hutun karatu da aka amince mata.
A cewar jami’ar, an dauki Dr. Kamal aiki ne a ranar 25 ga Mayu, 2018, a matsayin Malama a Sashen Harhada Magunguna, Kwalejin Magunguna da Kimiyyar Lafiya.
Sanarwar ta kara da cewa daga baya an ba ta hutun karatu na shekaru biyu a Jami’ar Putra Malaysia don neman digiri na biyu (Master’s) a fannin Pharmacology da Toxicology, ƙarƙashin tsarin daukar nauyin kai amma tana karbar cikakken albashi.
Jami’ar ta ce an amince da wannan hutu ne duk da cewa ba ta cika lokacin da yawanci ake bukata don cancantar samun irin wannan gata ba, tana mai bayyana matakin a matsayin wani bangare na sadaukarwar jami’ar wajen habaka ilimin ma’aikatanta.
Kafin ta tafi karatun, an ba da rahoton cewa Dr. Kamal ta sanya hannu a kan Yarjejeniyar Hutun Karatu (Study Fellowship Bond) wanda ke bukatar ta dawo jami’ar bayan ta kammala karatunta don ta yi aiki na tsawon lokacin da ya dace da ma’aikatan da suka ji dadin karbar albashi lokacin hutun karatunsu.
SolaceBase ta ruwaito cewa FUD ta ce daga baya ta amince da tsawaita hutun karatun nata, inda ta mayar da ranar da ake sa ran za ta dawo bakin aiki zuwa 10 ga Nuwamba, 2022.
Jami’ar ta ce: “Duk da wannan tsawaitawar, Dr. Kamal ba ta dawo bakin aiki ba bayan cikar wa’adin da aka amince da shi.”
Ta bayyana cewa biyo bayan binciken tantance ma’aikata da aka gudanar a shekarar 2024, an umarci Dr. Kamal a hukumance da ta dawo bakin aiki, amma maimakon haka, sai ta nemi a dakatar da wajibcin da ke kanta na Yarjejeniyar Hutun Karatu.
A cewar jami’ar, an yi la’akari da bukatar amma aka yi watsi da ita, inda Shugaban Sashen Pharmacology ya shawarce ta da ta dawo kuma ta bi ka’idojin yarjejeniyar.
Jami’ar ta ce daga baya ta fara tsarin horo na cikin gida bayan da ta ci gaba da zama ba tare da ta dawo bakin aiki ba.
Ta ce an aika wa Dr. Kamal takardar gayyata don amsa tambayoyi na hukuma, wanda ta amsa da cewa tana kasar Amurka tana jiran takaddun zama da za su ba ta damar gudanar da karin horon kwararru a fannin Clinical Pharmacology.
FUD ta nanata cewa an ba Dr. Kamal dama don daidaita matsayarnta, ciki har da tattaunawa ta yanar gizo a gaban Kwamitin Bincike har sau biyu.
Jami’ar ta ce an shawarce ta yayin zaman da ta dawo jami’ar kuma ta bi sahun duk wata bukata ta hanyoyin gudanarwa da suka dace, amma ta kasa yin hakan.
Daga baya an mika batun zuwa Kwamitin Horo na Manyan Ma’aikata (SSDC), wanda a cewar jami’ar, ya gayyaci Dr. Kamal sau biyu don ta bayyana ta kare kanta.
“Ba ta amsa waɗannan gayyatar ba.”
Bayan haka, SSDC ta yi la’akari da bayanan da ke akwai kuma ta ba da shawarwari ga Hukumar Gudanarwa daidai da dokokin jami’ar.
Jami’ar ta kuma bayyana cewa kwamitin ya umarci Bursary da ya lissafta albashin da aka biya Dr. Kamal a tsawon lokaci, inda aka kiyasta kudin a kan Naira 16,375,817.
FUD ta kara da cewa Hukumar Gudanarwa ta ba da umarnin cewa a sanar da hukumomin da suka dace, ciki har da ofishin jakadancin kasar da take zaune da sauran hukumomi, game da shawarar da jami’ar ta yanke.
A kan wallafar da sunan Dr. Kamal, jami’ar ta ce an fitar da ita ne a matsayin wani bangare na matakan gudanarwa game da jami’an da suka kasa cika wajibai da suka samo asali daga hutun karatu da aka amince da su.












































