Shugaban Hukumar Kudaden Shiga ta Kasa (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana takawa da kafa zuwa ofishinsa kuma sau daya kacal yake cin abinci a rana, inda ya musanta zargin cewa shugaban na gudanar da rayuwar almubazzaranci.
Adedeji ya yi wadannan kalaman ne a ranar Lahadi yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi game da salon rayuwar ma’aikatan gwamnati a daidai lokacin da Najeriya ke cikin mawuyacin halin tattalin arziki.
Shugaban na NRS ya kare salon rayuwar Tinubu a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fama da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki, da kuma tattaunawa mai zafi da ake yi kan kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma yadda jami’an gwamnati ke rayuwa.
A cewar Adedeji, yawancin lokuta Tinubu yana takawa ne da kafa daga gidansa zuwa ofis, yana amfani da mota ne kawai idan zai tafi filin jirgin sama, inda kuma kara da cewa shugaban yana cin abinci sau daya ne kacal a rana, sannan bai taba fita kasar waje ba a cikin watanni uku da suka gabata.
An kuma tambayi shugaban na NRS game da rahotannin dake nuna yawan motocin alfarma na “Escalade” da ake zargin suna cikin ayarin motocin Tinubu.
Yayin da yake mayar da martani, Adedeji ya nuna shakku kan dalilin wannan damuwar, inda ya bayyana cewa shugaban kasa yana da karfin sayen irin wadannan motocin, saboda haka kada a rika nuna shi a matsayin mai rayuwar barna saboda amfani da su.
“Shugaban kasa yana tafiya ofis ne a kasa daga gidansa, ba ya ma tuki sai dai idan zai tafi filin jirgin sama. Ban san a ina kuke ganin ayarin motocin ba. Kafin ya zama shugaban kasa wace mota yake hawa?
“Nawa ne kudin Escalade da har shugaban Najeriya ba zai iya saya ba? Don Allah kada ku kunyata wannan kasa.
“Mene ne ma’anar rayuwar kasaita? A watannin baya ma bai bar kasar nan ba, yana ta tafiya a kasa da aiki. Idan ka je can yanzu, za ka gansu yana duba wannan takarda ko waccan.
“To mene ne rayuwar kasaita? Shugaban kasa yana cin abinci sau daya a rana. Bukukuwa nawa kuka ganshi a cikinsu a cikin shekaru uku da suka gabata? Guda nawa kuka gani, ko a hutu ko a ina?”












































