Gwamnatin Jihar Kano ta mika makarantar School of Rural Technology and Entrepreneurship Development da ke Rano, ga Kwamitin Gudanarwa da ke kula da kafa Sabuwar Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Rano.
Sanarwar ta fito daga Kakakin Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Lahadi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya jagoranci bikin mika makarantar a karshen makon da ya gabata, inda ya gana da mambobin Kwamitin Gudanarwar tare da zagayen duba kayayyakin da za a fara amfani da su wajen gina sabuwar makarantar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ba da cikakken goyon baya domin tabbatar da cewa an fara aikin makarantar akan lokaci ba tare da cikas ba.
Ya kara da cewa ilimin fasaha da koyon sana’o’i suna da matukar muhimmanci wajen shirya matasa su samu aikin yi, su zama ‘yan kasuwa, masu dogara da kansu.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta gyara da bunkasa kayayyakin da ke sabon wurin makarantar da ke Karamar Hukumar Sumaila domin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa.
Ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sanata Kawu Sumaila da Hon. Kabiru Alhassan Rurum bisa jajircewarsu wajen ganin an kafa wannan Kwaleji.
Haka kuma ya yaba wa mambobin Kwamitin Gudanarwa bisa sadaukarwa da kokarin da suka yi wanda ya kawo aikin kusa da farawa.
A jawabinsu, Sanata Kawu Sumaila da Hon. Rurum sun gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da kafa makarantar da kuma Gwamna Yusuf bisa goyon bayansa.
Sun ce suna da yakinin cewa wannan cibiya za ta bude kofa ga matasa da dama su koyi sana’o’i da ilimin fasaha, kuma za ta kawo ci gaba ga Jihar Kano da kewayenta.
A nasa bangaren, Sanata UK Umar wanda ke cikin Kwamitin, ya roki gwamnati da ta kara bai wa makarantar fili domin fadada ta a gaba da kuma samun sarari na gine-ginen karatu da na tallafi.













































