Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zabi Alhaji Ibrahim Augie a matsayin abokin takararsa na zaben gwamnan 2027, inda ya sauya Mataimakin Gwamna na yanzu, Sanata Umar Tafida.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na X a ranar Lahadi ta ce Sakataren Tsare-Tsare na Jam’iyyar APC Alhaji Suleiman Argungu ne ya sanar da wannan matsaya a Birnin Kebbi
A cewar sanarwar, Argungu ya ce an dauki wannan shawara ne bisa shawarar kwararrun lauyoyi dangane da cancantar Mataimakin Gwamna na yanzu.
“An cire Mataimakin Gwamna na yanzu a matsayin abokin takarar Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu na zaben 2027 bisa shawarar lauyoyi.” in ji shi.
Ya ce an cimma wannan shawara ne da yardar Tafida da kuma amincewarsa, inda ya jaddada cewa babu sabani tsakanin gwamna da mataimakinsa.
Bayan haka Argungu ya sanar da Augiea matsayin sabon abokin takarar Idris na zaben gwamnan 2027.
Ya yi kira ga ‘yan siyasa, mambobi da magoya bayan APC a fadin jihar da su karɓbi wannan sauyi tare da yin aiki tare domin samun nasarar jam’iyya a zaben 2027.
Gwamna Idris ma ya musanta duk wata magana da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da Tafida.
Gwamnan ya yi kira da a ci gaba da hada kai, goyon baya da hadin gwiwa yayin da
gwamnatinsa ke kokarin kawo karin ci gaba a Jihar Kebbi.
Augie tsohon Kwamishinan Kudi ne a Jihar Kebbi a gwamnatin tsohon Gwamna Atiku Bagudu, kuma dan Asalin Ƙaramar Hukumar Augie ne a jihar.













































