Rundunar ’Yan sanda ta Jihar Kogi ta kama wani mutum mai shekara 33, Jacob Irewa, bisa zargin sa da kona matarsa da wuta yayin wata daddamar iyali.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a 14 ga Agusta, a rukunin gidaje na Oworo da ke Felele a garin Lokoja, a cewar Jami’ar Hulda da Jama’a ta Rundunar ’Yan sandan, ASP Afusat Saliu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a Lokoja, Saliu ta bayyana cewa wadda abun ya rutsa da ita, Sunusi Berida Irawo, ta sami raunuka kuma tana karbar magani a Asibitin Honey Gold da ke Felele.
Ta ce jami’an binciken sirri na bangaren ‘Division B’ da ke Felele sun amsa kiran gaggawa inda suka kama wanda ake zargin dumu-dumu a wurin da lamarin ya faru.
“Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa ce-ce-ku-cen ya fara ne bayan da Mrs Irawo ta kona wasu tufafin mijinta ba tare da amincewarsa ba.
“Rikicin ya fara tsamari ne yayin da wanda ake zargin ya yi wa matarsa barazana, inda ya debo fetur daga cikin babur dinsa ya zuba mata ya kuma cinna mata wuta.
“A cikin bayanan da ya ba ’yan sanda, wanda ake zargin ya amsa laifin kona matarsa,” in ji Saliu.
Kakakin ’yan sandan ta ce an fara gudanar da gamsasshen bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya auku da kuma tattara cikakkun shaidu.
Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar, CP Naziru Kankarofi, ya yi Allah wadai da lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin rashin imani da abin da ba za a taba amincewa da shi ba.
Ya nanata cewa rundunar ba za ta taba kyale duk wani nau’i na cin zarafi ba, musamman ma na cikin gida, sannan ya yi kira ga mazauna yankin da su rika warware sabani ta hanyoyin shari’a.
“Rundunar ‘Yansanda ba za ta kyale duk wani mataki da zai iya jefa rayukan mutane cikin hadari ba.
“Muna shawartar ‘yan kasa da su nemi hanyoyin lumana da na shari’a wajen daidaita rashin fahimta,” in ji Kankarofi.
’Yan sandan sun ce za a tuhumi Irewa da laifin yunkurin kisan kai da gangan bayan an kammala bincike.
Rundunar ta sake tabbatar wa mazauna jihar kudurinta na kare rayuka da dukiyoyi gami da mika wadanda suka aikata manyan laifuka gaban shari’a.
Haka kuma, ta bukaci mambobin al’umma da su rika bayar da rahoton duk wani lamari na cin zarafi na cikin gida da gaggawa domin hana girmamar lamarin. (NAN)













































