BBC ta nada sabon editan sashen Hausa

IMG 20260904 WA0343 750x430

Hukumar yada labarai ta BBC ta nada Haruna Ibrahim Kakangi a matsayin sabon Editan sashen Hausa.

SolaceBase ta ruwaito cewa Juliet Njeri, Shugabar BBC ta Africa, ce ta sanar da nadin da misalin karfe 3:30 na yammacin ranar Juma’a a wani sako da ta aike wa ma’aikatan BBC.

A cewar Njeri, Kakangi ne ya yi nasara bayan an gudanar zagayen tantancewa har biyu, kuma zai yi aiki a matsayin edita na tsawon shekara daya.

Nadin nasa na zuwa ne kimanin shekara daya bayan murabus din tsohon editan sashen, Aliyu Tanko, wanda ya yi ritaya daga mukamin a watan Agustan 2025 bayan ya rike shugabancin BBC Hausa tun shekarar 2020.

Murabus din Tanko ya faru ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar da zarge-zargen cin zarafi da cin mutuncin ma’aikata gami da gudanar da bincike na cikin gida a BBC.

Sai dai, a wancan lokacin, Tanko ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda wasu dalilai na kashin kai, kuma ya musanta cewa barin nasa na da alaka da wadannan zarge-zargen

Kakangi, wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, ya kammala digirinsa na farko a fannin Harshen Hausa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2008, sannan ya sami babban difloma a bangaren aikin jarida daga dai jami’ar a shekarar 2019.

Ya yi aiki da sashen BBC Media Action kafin daga baya ya koma Sashen Hausa na Gidan Rediyon Faransa.

Ya sake komawa BBC a shekarar 2017 bayan ya yi nasara a neman aikin da ya yi, inda ya zama cikakken ma’aikacin Sashen Hausa na BBC.

Bayan komawarsa BBC, Kakangi ya yi aiki a matsayin babban dan jarida a kan wani shiri na hadin gwiwa tsakanin BBC da gidauniyar MacArthur Foundation.

Daga baya ya zama Shugaban Shaftukan Sada Zumunta na BBC Hausa, inda yake da alhakin kula da ayyukan sashen a kafofin sadarwa na zamani daban-daban.

Haka kuma, Kakangi ya halarci horar ta kwararrun ‘yan jarida na tsawon watanni biyu a cibiyar World Press Institute da ke Amurka, wanda hakan ya kara fadada gogewarsa a fannin rahotanni da sauran fannonin aikin jarida.

Wannan nadi ya zama wani babban mataki a aikinsa na jarida a BBC, kuma ya dora shi a matsayin jagoran daya daga cikin manyan rassan harsunan Afirka na BBC, wanda ke hidima ga miliyoyin masu jin harshen Hausa a Najeriya da sauran sassan duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here