Alkaliyar Amurka ta soki matakin korar ƴan Najeriya da Gambiya zuwa Ghana

US Judge 750x430

Wata alkaliyar kotun tarayya a Washington DC, Tanya Chutkan, ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta kori ’yan Najeriya da Gambiya zuwa Ghana.

Alkaliyar ta yi wannan magana ne bayan lauyoyin da ke kare wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun bayyana damuwa cewa idan aka mayar da su kasashensu, za su iya fuskantar azabtarwa ko tsangwama.

Labari mai alaƙa: Amurka ta kora ƴan Najeriya, Gambiya da wasu kasashen Yammacin Afrika zuwa Ghana

Chutkan ta umurci gwamnatin Amurka da ta gabatar da cikakken bayani kan hanyoyin da ta tanada don tabbatar da cewa Ghana ba za ta maida su gida ba, inda ta ce yarjejeniyar ta yi kama da kauce wa dokokin shige da fice na Amurka.

Sai dai duk da wannan suka, alkaliyar bata yanke hukunci a kan masu ƙorafin ba, tana mai cewa hukuncin nata na iya zama marar amfani idan kotun koli ta dakatar da shi nan take.

Rahoton ya nuna cewa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun shigar da ƙara, inda suka bayyana yadda aka kwashe su daga gidan gyaran hali na Louisiana, aka daure su sannan aka saka su a cikin jirgin soja na Amurka ba tare da sanin inda ake kaisu ba.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta ACLU da Asian Americans Advancing Justice suka mara musu baya.

Sai dai Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce ba ta da alhakin su tunda an riga an mika su Ghana, tana mai jaddada cewa kotu ba ta da ikon shawo kan irin wannan hukuma ta diflomasiyya.

A cewar gwamnatin Ghana, ta amince da yarjejeniya da Amurka don karɓar wasu ’yan ƙasashen Yammacin Afirka da aka kora, inda shugaban ƙasar John Mahama ya tabbatar da cewa mutane 14 sun riga sun iso ƙasar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here