Gwamnatin Birtaniya ta yabi Kano kan matsayinta a fannin kashe kudi a harkar ilimi

Abba Abba Abba 585x430 1

Gwamnatin Birtaniya ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bayan jihar ta fito a matsayin gwamnatin jiha mafi fice wajen kashe kudi a fannin ilimi a fadin Afirka ta Yammaci.

Wannan na cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin-Tofa, Daraktan yada labaran Gwamna Abba Yusuf ya fitar a Kano ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Mista Ian Attfield, Babban Mashawarci kan Ilimi a Ofishin Jakadan Birtaniya a Najeriya ne ya yi wannan yabo a shafinsa na X.

Ya ce Attfield ya bayyana wannan karramawa a matsayin babban nasara ga jihar kuma alama ce da ke nuna aniyar gwamnatin na ba da fifiko ga bangaren ilimi a matsayin ginshikin cigaba mai dorewa.

A cewar Dawakin Tofa, wannan yabo ya biyo bayan fitar da Ma’aunin Kashe Kudi a Harkar Ilimi na Jihohi na Shekarar 2026 da Cibiyar WAESI ta fitar.

Wannan wani yunkuri ne na manufofin gidauniyar Afirka ta Cité Internationale Universitaire de Paris da aka tsara domin inganta shugabancin na gari bisa hujjoji wajen samar da kudade ga harkar ilimi a cikin kasashe 15 na ECOWAS da gwamnatoci 209 na jihohin da ke cikin kasashen.

Ya ce a cikin wata sanarwa a hukumance da aka aike wa Yusuf, masu bada lambar yabo sun sanar da cewa Jihar Kano ta zo a mataki na farko daga cikin dukkanin gwamnatocin jihohi a Yammacin Afirka.

Wannan ya ba ta lakabin “Babbar Gwarzuwa Mai Daukar Nauyin Ilimi” a matsayin Gwamnatin Jiha Mafi Fice a Afirka ta Yammaci ta shekarar 2026.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here