Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta kasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar (SSCE) ta 2025, inda kashi 60.26 cikin 100 na ɗalibai suka samu Credit biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.
Yayin da yake bayyana sakamakon a hedikwatar hukumar da ke Minna, babban birnin Jihar Neja a ranar Laraba, shugaban hukumar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce, yawan ɗaliban da suka samu Credit biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi sun kai 818,492, wanda ya kai kashi 60.26 cikin ɗari.
Haka kuma, Farfesa Wushishi ya bayyana cewa, yawan ɗaliban da suka samu Credit biyar a darussa daban-daban, ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba, ya kai 1,144,496, wanda ya kai kashi 84.26 cikin ɗari.
Ya ƙara da cewa, adadin ɗaliban da suka yi rajista domin rubuta jarabawar ya kai 1,367,210, inda maza suka kasance 685,514 yayin da mata suka kasance 681,696.
Amma yawan waɗanda suka zauna jarabawar ya kasance 1,358,339, inda maza suka kai 680,292 sai mata 678,047.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan nasarar ɗaliban da kuma ƙalubalen da ke fuskantar tsarin ilimi a Najeriya.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da inganta gudanar da jarabawa domin tabbatar da sahihancin sakamakon.
Rahoton ya kuma nuna cewa, NECO na shirin fitar da ƙarin bayanai nan gaba game da jarabawar, ciki har da yawan waɗanda aka kama da laifin rashin gaskiya a jarabawa da matakan ladabtarwa da za a ɗauka.













































